Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya kasance cikin manyan mutanen da aka fi danganta da aikata manyan laifuka da cin hanci da rashawa, a cewar wani rahoto daga Cibiyar Organized Crime and Corruption Reporting Project (OCCRP).
OCCRP ta saba gudanar da zaɓen shekara-shekara, inda ta nemi ‘yan jarida, ƙwararru, da sauran masu ruwa da tsaki su kaɗa ƙuri’a don tantance mutanen da suka fi aikata laifuka a fannin cin hanci da rashawa.
A sakamakon wannan shekara, Tinubu ya zo na uku a jerin. Tsohon Shugaban Syria, Bashar al-Assad, ya kama matsayi na ɗaya saboda abubuwan da suka shafi ƙasar a baya-bayan nan, kamar yadda OCCRP ta bayyana.
Shugaban Kenya, William Ruto, ya zo na biyu a jerin, duk da cewa shi ne ya fi kowa samun ƙuri’u fiye da 40,000.
Cibiyar ta kuma bayyana cewa ta ƙaddamar da “lambar zambo ta rayuwa” ga Shugaban Ƙasar Equatorial Guinea a matsayin shugaba mafi daɗewa kan mulki a duniya, wanda ya shafe sama da shekaru goma yana jagorancin ƙasar.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj
