Wani Gagararren Zaki ya Kashe Maikula Da Shi A Gidan Zoo Na Obasanjo

IMG 20240929 WA0078

Daga Aminu Bala Madobi

Bayanai sun ce an cire gawar wanda aka kashe tare da kai ta dakin ajiya a babban asibitin Ijaye.

Alfijir labarai ta rawaito wani al’amari da ya wakana yayin da wani murgujejen zaki ya murkushe tare da kashe wani ma’aikacin gidan namun daji mai shekaru 35 na Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta.

Rahotanni sun ce tuni rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta tabbatar da faruwar lamarin a karshen mako bayan faruwar lamarin.

An ce ma’aikacin dakin ajiyar zakin haifaffen jihar Bauchi mai suna Babandi Daule ya manta bai datse makullai da shingen zakin ba kafin ya tunkari kejin don ciyar da dabbar.

An bayyana cewa hakan ya baiwa zakin damar tserewa tare da kai hari ga ma’aikacin, wanda ya yi sanadin raunuka a wuyansa, kuma daga bisani ya kashe shi har lahira.

Bayanai sun ce an cire gawar wanda aka kashe tare da kai ta dakin ajiya a babban asibitin Ijaye.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan wata dabbar gidan ajiya mai suna Hippo ta kashe wani mai kamun kifi ɗan shekaru 60, Malam Usman Maigadi, a ranar Lahadi a kogin Yauri dake jihar Kebbi.

Maigadi, wanda ya yi aiki a matsayin mai gadi a gonar Sarkin Yauri’s Orchard Farm, yana kamun kifi ne lokacin da dabbar ta kai masa hari, akokarin da take na kare ‘ya’yanta.

Shugaban karamar hukumar Yauri, Alhaji Abubakar Shu’aibu ya tabbatar da jana’izar Maigadi.

Ya ce, “An yi jana’izar Maigadi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a Yauri, bayan an yi sallar jana’iza.”

A wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran sa Alhaji Ahmed Idris ya fitar, gwamna Nasir Idris ya mika ta’aziyya ga masarautar Yauri da iyalan Maigadi.

“Ina son Masarautar da yan uwa da iyalan marigayin su jajirce wajen amincewa da nufin Ubangiji cikin aminci.

“Ina rokon Allah ya gafartawa marigayin ya kuma saka masa Jannatul Firdaus,” in ji gwamnan.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *