An sami rudani a jihar Gombe a ranar Kirsimeti yayin da wani direban motar haya da ya kasa sarrafa motarsa inda ya kunna kai masu bikin Kirsimeti.
Alfijir labarai ta rawaito masu bikin Kirsimeti din suna cikin wani jerin gwano daga unguwar Tumfure zuwa gidan gwamnatin jihar da fadar Sarkin Gombe don kai ziyara, lokacin da lamarin ya faru.
Mutane kimanin 22 daga cikin masu bikin Kirsimeti din sun jikkata a hatsarin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Gombe, Buhari Abdullahi, da ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitin koyarwa na tarayya dake Gombe da kuma Asibitin Kwararru don samun kulawa.
Sai dai, Abdullahi ya ce kawo yanzu babu wanda ya rasa ransa al’amarin.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj
