Shugaban ƙasar Bangladesh, Mohammed Shahabuddin, ya yi murabus daga muƙaminsa saboda matsanancin rashin lafiya, lamarin da ya kawo ƙarshen wa’adinsa na shekaru biyar kafin lokacin da aka tsara ya cika.
Rahotanni sun bayyana cewa Shahabuddin ya yanke shawarar sauka daga kan mulki ne sakamakon matsalolin lafiya da suka hana shi ci gaba da gudanar da manyan ayyukan ofishinsa yadda ya kamata.
Jaridar Alfijir labarai ta rawaito cewar murabus ɗin nasa ya janyo sabon babi a siyasar kasar Bangladesh, inda ake sa ran hukumomin ƙasar za su bi tanadin kundin tsarin mulki wajen cike gurbin shugaban ƙasar da kuma tabbatar da ci gaba da gudanar da mulki cikin lumana.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
