Daga Aminu Bala Madobi
Wasu shuwagabannin ‘yan bindiga waɗanda suka addabi yankin Batsari, Safana da Jibia a jihar Katsina, sun miƙa wuya tare da aje makamansu bayan gumurzu da sojoji, domin rungumar zaman lafiya.
Rahotonni sunce shuwagabannin ‘yan bin-digar da suka miƙa wuya, sun hada da ƙasurgumin dan fashin daji, Abu Radda, Umar Black da Abdullahi Lanƙai, Jijjige da kuma dabar Musa Ɗan gandu daga yankin garin Jibia a Katsina.
A cikin jawaban tubabbun ‘yan bindigar sun nemi gwamnati ta duba bukatunsu wajen gina masu kasuwanni da asibitoci da kuma samar musu da ruwan sha, domin yin rayuwa mai inganci.
A yayin zaman kungiyar mutanen yankin da matsalar tsaro ta shafa karkashin jagorancin Comrd Hamisu S Batsari, sune suka wakilci al’ummar da matsalar tsaron ta shafa a yankunan.
A karshe, shuwagabannin ‘yan bin-digar sun miƙa makamansu ga sojojin, inda suka sako wasu mutanen da suka yi garkuwa da su tare da ɗaukar alkawarin rungumar zaman lafiya.


Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ
