Daga Aminu Bala Madobi
’Yan Majalisar Dokokin Jihar Filato wadanda kotun daukaka kara ta kwace kujerunsu sun lashi takobin dowawa bakin aiki.
Alfijir labarai ta rawaito ranar Litinin ’yan majalisar dokokin jihar PDP 16 da kotun daukaka kara ta kwace kujerunsu, sun lashi takobin ci gaba da aiki daga ranar Talata.
Kotun daukaka kara ta kwace kujerunsu ne a bisa hujjar cewa jam’iyyarsu ba da ta da halastaccen shugabanci da zai tsayar da ’yan takara a zaben 2023.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da suka fitar ga manema labarai a Jos ranar Litinin .
Ishaku Maren Mai magana a madadinsu ya ce hukuncin Kotun Koli da ya tabbatar da nasarar Gwamna Caleb Mutfwang na jami’yyar ya nuna cewa su ne halastattun ’yan majalisar.
Rukunin yan majalisar suka ce za su dawo majalisar a ranar Talata da majalisar za ta dawo daga hutun wata biyu da ta je.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V
