Daga Mai Wanke Motoci Zuwa Matashin Ɗan Kasuwa a Duniyar Kasuwancin Motoci ta Intanet

IMG 170144 161026 1792166515388

Tarihin jajircewa, gaskiya, aiki tuƙuru, riƙon amana da hangen nesa.

ZAKI MOTORS KANO NIG. LTD kamfani ne na kasuwancin motoci ta Intanet, mallakar matashin ɗan kasuwa mai taso wa, Aliyu Abdullahi Aliyu, wanda tarihinsa ya nuna yadda jajircewa, haƙuri da dagewa za su iya sauya rayuwar mutum daga ƙaramin matsayi zuwa cikar babban buri.

Tafiyarsa ta fara ne a kusan shekarar 2013, a kan titin Abdullahi Bayero da ke Kano, inda ya ke aiki a matsayin mai Wanki da goge motoci, goge da kuma kai saƙo.

Duk da irin ƙalubalen da ya ke fuskanta a wannan lokaci, Aliyu bai daina ƙoƙarin ganin burinsa ya cika ba. Ya ci gaba da nuna gaskiya, aiki tuƙuru, riƙon amana da jajircewa a duk ayyukan da ya ke yi.

Saboda lura da ƙwazonsa da halayensa na gari, ɗaya daga cikin kamfanonin da ya ke aiki da su, ZAKI AND BROTHERS, ya ba shi damar zama sakatare. Wannan dama ta zama wani muhimmin mataki a rayuwarsa, domin ta ƙara masa ƙwarewa da damar ci gaba da gina burinsa a harkar motoci.

A kusan shekarar 2016, Aliyu ya fito da wani sabon tunani na buɗe shafukan sada zumunta domin tallata kamfanin da ya ke aiki da shi tare da isar da tallace-tallacen motoci ga jama’a da dama. Wannan tunani ne ya haifar da kafuwar ZAKI MOTORS KANO, wadda ta bi hanyoyin rajista da suka dace, kuma a wancan lokaci kamfanin na da alaƙa da ZAKI AND BROTHERS saboda kasancewarsa sakatare a kamfanin.

Ci gaban ZAKI MOTORS KANO

A yau, ZAKI MOTORS KANO ya zama kamfanin kasuwancin motoci ta Intanet da ke kan Abdullahi Bayero Road, Kano. Kamfanin ya na taimaka wa masu sayen motoci, masu sayar da motoci da dillalan motoci ta hanyar haɗa su da juna da kuma tallata motocinsu ta kafafen sada zumunta.

Ayyukan da kamfanin ke bayarwa sun haɗa da Bidding, shigo da motoci daga ƙasashen waje, clearance watau biyan kuɗin fito, da tallata motocin masu su da dillalai. Haka kuma, kamfanin ya na ɗaukar hotunan motoci tare da wallafa su a kafafen sada zumunta domin taimaka wa masu motocin samun masu saye.

Ɗaya daga cikin abubuwan da suka bambanta ZAKI MOTORS KANO da takwarorinsa shi ne yadda ya ke taimaka wa masu motoci da dillalai ta hanyar ɗaukar hotunan motocinsu da tallata su kyauta. Ba a cajin kuɗin tallata mota ko ɗaukar hotonta, sai dai idan mai motar ya ga dama ya ba da wani abu domin godiya ga aikin da aka yi masa.

Haka kuma, kamfanin ya na taimaka wa wajen haɗa masu saye da masu sayar da motoci, kuma a wasu lokuta ya na ƙara nasa ribar a kan farashin da dillali ya bayar, gwargwadon tsarin cinikin da aka amince da shi.

Babbar nasara a kafafen sada zumunta

ZAKI MOTORS KANO ya gina babbar nasara a kafafen sada zumunta, inda ya ke da mabiya kamar haka:

Facebook: Mabiya 550,000

Instagram: Mabiya 145,000

TikTok: Mabiya 136,000

Snapchat: Mabiya 122,000

X (Twitter): Mabiya 4,000

 

Kamfanin ya na kuma ƙoƙarin bunƙasa shafinsa na YouTube. Idan aka haɗa mabiya a waɗannan kafafe, adadin ya haura mutum miliyan ɗaya, abin da ke nuna irin faɗaɗar tasirin kamfanin a harkar tallata motoci ta Intanet.

 

Sabuwar hanya ta tallata motoci a Kano

ZAKI MOTORS KANO ya zo da wata sabuwar hanya ta tallata motoci a Kano, ta hanyar amfani da fasahar zamani da kafafen sada zumunta wajen haɗa masu motoci, dillalai da masu son sayen motoci. Wannan tsari ya na bai wa dillalai damar nuna motocinsu ga jama’a masu yawa, tare da taimaka wa masu saye wajen samun motocin da su ke nema cikin sauƙi.

 

Daga wanke motoci da goge su zuwa gina kamfanin kasuwancin motoci ta intanet, tarihin Aliyu Abdullahi Aliyu ya na nuna cewa, ƙaramin matsayi a farkon rayuwa ba ya hana mutum cimma babban buri idan ya kasance mai gaskiya, jajircewa da dagewa.

 

ZAKI MOTORS KANO ba kamfanin kasuwancin motoci kawai ba ne; kamfani ne na zamani da aka gina shi bisa amana, jajircewa, hangen nesa da imani da cewa fasahar Intanet za ta iya sauya harkar kasuwancin motoci.

 

📢 KU BI ALFIJIR LABARAI

 

Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sahihan labarai, rahotanni, bincike da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da duniya.

 

📩 TUNTUƁA DA HAƊIN GWIWA

Kira/WhatsApp: +234 803 207 7835

 

🌐 KAFAFEFENMU

X: https://twitter.com/Musabestseller?s=09

Facebook: https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

Threads: https://www.threads.net/@alfijirlabarai

YouTube: https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Instagram: https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

📲 WhatsApp Group:

https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f

 

ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES

Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce

 

© 2026 Alfijir Labarai Media Services

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *