Gwamnatin Kano Ta Raba Filaye Ga Masu Taimakawa Gwamna SSR, SR, Da SA Sama da 2,500

IMG 222626 01826 1785619594158

Gwamnatin Kano ta fara raba takardun filaye ga mataimaka na musamman g Gwamnan kusa Alh Abba Kabir Yusuf sama da 2,500, SR, SSR, SA,

Kwamishinan Filaye da Tsare-tsaren Birane, Abduljabbar Muhammad Umar Garko, ya ce shirin na da nufin taimaka wa waɗanda suka amfana su mallaki gidaje, tare kuma inganta tsarin gine-gine a jihar. Ya kuma gargaɗe su da kada su sayar da filayen ko su bari masu kwace filaye su karɓe su.

Garko ya ce an tsara wuraren da aka ware filayen tare da samar da muhimman abubuwan more rayuwa kamar masallatai, makarantu, tashoshin kashe gobara da wuraren tsaro. Ya ƙara da cewa gwamnati na sabunta tsarin kula da filaye ta hanyar amfani da fasahar zamani a Ma’aikatar Filaye da Tsare-tsaren Birane da kuma KANGIS.

A nasa jawabin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Umar Faruk Ibrahim, wanda ya wakilci gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce rabon filayen na daga cikin matakan gwamnati na inganta jin daɗin ma’aikata da ƙara damar mallakar filaye. Ya ce gwamnati ta kuma aiwatar da wasu shirye-shirye a fannonin ilimi, hanyoyi, noma, ruwa, gidaje da gyaran tsarin mallakar filaye.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *