Gwamnatin Kano ta hana duk wata hada-hadar kasa a ciki da wajan kadarorinta wanda ya hada da makarantu, da Asibitoci da sauransu

PXL 20260803 115504573

Gwamnatin jihar Kano ta haramta duk wata hada-hadar filaye a ciki da wajen kadarorinta, ciki har da makarantu, asibitoci da sauran wuraren gwamnati, domin kare kadarorin al’umma daga mamaya da sayarwa ba bisa ka’ida ba.

Kwamishinan Ma’aikatar Ƙasa da Tsare-tsaren Birane ta Jihar Kano, Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar, ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyarar duba Makarantar Sakandiren Yan Mata ta WTC tare da dakatar da wasu gine-ginen da aka fara yi ba tare da bin Æ™a’ida ba.

Ya ce gwamnatin jihar ta gano cewa an raba filaye sama da 100 a harabar makarantar domin gina gidajen kwana, lamarin da ya sa gwamnatin ta É—auki matakin dakatar da duk wata irin mu’amala da filayen kadarorin gwamnati.

A cewarsa, bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf, an haramta yanka ko sayar da duk wani fili da ke cikin kadarorin gwamnatin Kano, musamman makarantu, asibitoci da sauran wuraren gwamnati.

Kwamishinan ya gargaÉ—i masu saye da masu sayar da irin waÉ—annan filaye da su guji shiga irin wannan harka, yana mai jaddada cewa gwamnati za ta bi hanyar doka domin hukunta duk wanda aka samu da hannu a lamarin.

A nasa jawabin, shugaban kwamitin da gwamnatin Kano ta kafa domin kawar da gine-ginen da aka yi ba bisa Æ™a’ida ba, kuma Shugaban Hukumar KINGIS, Dakta Dalhatu Aliyu Sani, ya ce matakin ya nuna Æ™udirin gwamnatin jihar na kare kadarorin jama’a da tabbatar da bin doka.

A nata bangaren Shugabar Makarantar Sakandiren ‘Yan Mata ta WTC, Hajiya Uwani Ahmad Balarabe, ta yaba da ziyarar da kwamishinan ya kai makarantar, tana mai cewa hakan ya Æ™ara musu Æ™warin gwiwa wajen kare kadarorin makarantar.

Abduljabbar ya sake tabbatar da cewa gwamnatin Kano ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kare kadarorinta da kuma ɗaukar matakan da suka dace kan duk wanda ya karya doka.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *