Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibitin Kwararru Na Best Choice Dake Kano 

IMG 084519 15826 1786779933312

Gwamna Alh Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar dubiya ne da kuma ganin yadda su kansu ma’aikatan asibitin suke kulawa da lafiyar al’ummar jihar Kano.

Ziyarar ta Gwamnan ta kasance ne a ranar juma’a cikin dare, a Irin bazatan da ya saba yi zuwa asibitocin gwamnati domin ganin yadda ake kulawa da lafiyar al’umma a wannan lokacin.

Bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya gama duba mara sa lafiya, kuma ya kewaye kowanne ɓangare na asibitin tare da rakiyar likitan dake kan aiki tare da ma’aikatansa a wannan daren.

Gwamnan kuma ya yaba da yadda yaga ma’aikatan wannan asibitin kwararru na Best Choice suke gudanar da ayyukan su na kula da lafiyar al’ummar jihar Kano.

Wannan ta nuna karara gwamna Alh Abba Kabir Yusuf ba wai iya abin da ya shafi mallakin gwamnati yake mayar da hankali a kai ba, har da abin da ya Shafi na ƴan kasuwa na al’ummar jihar, suma ya na basu mahimmanci domin cigaban jihar Kano baki daya.

A yayin ziyarar Gwamna ya godewa shuwagabannin asibitin Best Choice da ma’aikatan su, ganin yadda ya same su cikin dare kamar rana suna gabatar da ayyukan ceton rayukan al’umma. Sannan Gwamnan ya bawa Ma’aikatan kyauta ta musamman domin karin kwarin gwuiwar gudanar da ayyukan su.

Asibitin kwararru na Best Choice Specialist na nan a Tal’udu junction daura da makarantar Sheikh Al Rayyan da ke Kano, kuma suna gudanar da ayyukan cikin awanni 24/7 tare da kwararrun likitoci da ma’aikata a kowane sashe.

IMG 20260815 WA0279
Gwamna Yusuf da ma’aikatan Asibitin Kwararru Na Best Choice
IMG 083941 15826 1786779601731
Gwamna Yusuf da ma’aikatan Asibitin Kwararru Na Best Choice
IMG 083924 15826 1786779577191
Gwamna Yusuf da ma’aikatan Asibitin Kwararru Na Best Choice
IMG 083903 15826 1786779551499
Gwamna Yusuf da ma’aikatan Asibitin Kwararru Na Best Choice
IMG 20260815 WA0281
Gwamna Yusuf da ma’aikatan Asibitin Kwararru Na Best Choice

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *