Malaman Addinin Musulunci 500 sun goyi bayan Tinubu ya zarce a 2027

FB IMG 1787504797701

Mai ba shugaban kasa Bola Tinubu shawara kan harkokin siyasa da sauran al’amura, Ibrahim Masari, ya ce kusan malaman addinin Musulunci da shugabannin addini 500 daga jihohin Arewa 19 da Abuja sun amince da sake tsayawa takarar Tinubu a zaben shugaban ƙasa na 2027.

Masari ya bayyana hakan ne bayan halartar taron Northern Muslim Intellectual Forum da aka gudanar a Dutse, Jihar Jigawa.

Ya ce mahalarta taron sun tattauna matsalolin tsaro, tattalin arziki, ababen more rayuwa da ci gaban yankin Arewa, inda suka bayyana gamsuwa da matakan da gwamnatin Tinubu ke ɗauka.

A cewar Masari, mahalarta taron sun kada kuri’ar amincewa da Tinubu tare da kira ga ‘yan Najeriya, musamman al’ummar Arewa, da su goyi bayan sake zabensa da sauran ‘yan takarar jam’iyyar APC a 2027.

Taron ya samu halartar gwamnonin Jigawa, Kano, Yobe, Sokoto da Kaduna, da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, da Ministan Gidaje, Muttaka Darma.

Daily Nigerian

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

 

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

 

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

 

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

 

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *