Rimin Zakara: Mutane 80, Ne Suka Je DSS Domin a Tantancesu Cikin 500 Da Suka Nemi Diyya – Gwamnatin Kano 

IMG 174014 22826 1787416827659

Fiye da mutane 500 ne suka kai koke-kokensu Ma’aikatar Ƙasa da Tsare-tsaren Gine-gine ta Jihar Kano domin tantance ikirarin mallakar filayen da ake takaddama a kansu a Rimin Zakara, Ƙaramar Hukumar Ungogo, amma mutane 80 ne kawai suka kai matakin tantancewa na biyu a hukumar tsaro ta farin Kano DSS.

Kwamishinan Ma’aikatar Ƙasa da Tsare-tsaren Gine-gine, Abduljabbar Muhammad Umar Garko, shi ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a Kano ranar Asabar. Ya ce gwamnati ta raba aikin tantancewar zuwa matakai biyu domin hana zamba da ikirarin bogi.

Ya ce a matakin farko, masu neman diyya suna kai takardun da ke tabbatar da mallakarsu ma’aikatar domin tantance su. Daga nan ne ake tura su DSS domin ƙarin bincike, ciki har da tantance bayanan mutum ta hanyar na’urar zamani da ɗaukar yatsun hannu.

Kwamishinan ya ce tsarin na da nufin tabbatar da cewa kuɗin diyya sun isa ga haƙiƙanin masu filayen da aka tabbatar da mallakarsu. Ya kuma ce gwamnati na son daƙile zamba, ikirarin fili fiye da sau ɗaya da sauran hanyoyin da za su iya jawo biyan kuɗin gwamnati ga waɗanda ba su cancanta ba.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *