Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano kuma shugaban ma’aikata na tsohon shugaban jam’iyyar APC a Najeriya Mallam Muhammad Garba ya bayyana cewa jihar Kano a yau tana ganin tarun ayyuka da ake yi karkashin gwamnatin Abba Kabir Yusuf, don haka ‘yan jarida su rika ba da rahotanni dangane da ayyukan da gwamnatin ke yi.
Da yake jawabi a yayin sake bude ofishin wakilan kafafan yada labarai na Kano Correspondents’ Chapel Muhammad Garba yace “A ajiye siyasa a gefe tabbas Gwamna Yusuf na gudanar da ayyuka daban-daban da ake gani a zahiri, abin da ke nuna cewa gwamnatin ta karkata kan abubuwa da al’umma ke bukata.”
Da yake lale marhabun da bakin da suka halarci bikin sake sabunta ofishin shugaban kungiyar Murtala Adewale ya bayyana cewa Shugabancin kungiyar ya mayar da hankali wajen kula da walwala da kyautata yanayi da mambobi za su samu damar yin aiki.
“Ba kawai gyara ofishin bane batu ba,
samar da kyakkyawan yanayi da mambobin za su zauna a wajen mai kyawun yanayi a rika musayar bayanai da rika karbar baki na musamman, yanzu ne ma muka fara.” A cewar Adewale.
Bikin dai ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki kan abin da ya shafi aikin yada labarai da suka hadar da Farfesa Sule Ya’u Sule na sashin nazarin aikin jarida a Jami”ar Bayero da Hajiya Aishatu Sule shugabar tashar Muhasa Radio da sauran manyan baki da ‘yan jarida na ko wane bangare a Kano da Jigawa.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
