Ƙasarmu Ta Gado: Tattalin Arzikin Najeriya Ya Bunkasa da Kashi 4.43% a Kwata ta Biyu

FB IMG 1787320250002

Tattalin arzikin Najeriya ya samu ci gaba mafi girma a cikin kashi na biyu na shekarar 2026, inda ma’aunin tattalin arziki na GDP ya nuna ya ƙaru da kashi 4.43 cikin 100 idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar da ta gabata.

 

Sabbin alkaluman da Hukumar Kididdiga ta Ƙasa, NBS, ta fitar sun nuna cewa ci gaban na kashi na biyu ya fi na kashi na farko na shekarar, wanda ya kasance kashi 3.89 cikin 100.

 

Haka kuma, ci gaban kashi 4.43 cikin 100 shi ne mafi girma da tattalin arzikin Najeriya ya samu a cikin kwata guda tun daga kashi na biyu na shekarar 2021, lokacin da tattalin arzikin ya samu ci gaban kashi 5.01 cikin 100 bayan farfaɗowar da aka samu daga matsalar tattalin arziki ta annobar COVID-19.

Rahoton ya ce noma da harkokin sadarwa na daga cikin manyan abubuwan da suka taimaka wajen bunƙasar tattalin arzikin.

 

Noma ya samu gagarumin ci gaba musamman saboda ƙaruwar kiwon dabbobi. Samar da dabbobi ya ƙaru da kashi 6.92 cikin 100 a kashi na biyu na 2026, daga kashi 2.20 cikin 100 a kashi na farko.

 

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

 

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

 

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

 

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

 

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *