Shugaban Asibitin Kwararru na Best Choice dake Kano Auwal Lawal Muhammad (Dan Malikin Garo) ya taya gwamnan Kano Alh Abba Kabir Yusuf da al’ummar jihar Kano da ma Musulmin duniya murnar Maulidin Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama.
Lawal ya yaba wa gwamnan a kokarin sa na hada kan al’ummar jihar musamman abinda ya shafi addini domin magance rarrabuwar kawuna da fahimtar juna domin kawo zaman lafiya a fadin jihar.
Ya kara da cewar, lokaci ne da al’umma za suyi amfani da shi wajen kara neman kusanci da Allah tare da addu’oin neman zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin wannan ƙasa tamu da kuma jihar mu Kano baki daya
Shugaban Asibitin ya kuma yaba kan kokarin da gwamnan keyi na inganta fannin kiwon lafiya, inda ya bada misali da yadda Gwamnan ke gyarawa da inganta asibitoci, samar da kayan aikin likitanci na zamani, da horar da ma’aikatan lafiya.
Daga bisa kwamaret Auwal Lawan ya yaba wa gwamnan bisa sadaukarwa da tsantsar tausayi da yake nunawa, wadanda hakan ke tasiri a rayuwar al’umma.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
