Gwamnatin Tarayya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan jiragen sama na Nigeria Airways Bilyan 18 kuɗaɗen sallama daga aiki da suke ta Jira

FB IMG 1789166848901

Gwamnatin Tarayya ta fara biyan tsoffin ma’aikatan kamfanin jiragen sama na Nigeria Airways kuɗaɗen sallama daga aiki da suka daɗe suna jiran tsammani.

Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arziƙi, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa gwamnati za ta biya jimillar Naira biliyan 18 ga tsoffin ma’aikata 2,700.

Ya kara da cewa, zuwa yanzu an biya ma’aikata 2,100, yayin da aka amince da biyan wasu 600 da ke cikin rukuni na takwas da na tara.

Ministan ya ce ana biyan kuɗaɗen ne a rukuni-rukuni domin waɗanda aka kammala tantancewa kada su ci gaba da jira, yayin da ake tantance sauran masu neman haƙƙinsu.

Kuɗaɗen sun shafi ma’aikata manya da ƙanana, ba tare da bambanci ba. Ga waɗanda suka rasu kafin su karɓi haƙƙinsu, za a biya magadansu ko waɗanda doka ta amince da su bayan kammala matakan da suka dace. In ji ministan

Nigeria Airways ta daina aiki ne a shekarar 2003, kafin a kammala aikin rushe kamfanin a shekarar 2005.

Oyedele ya ce biyan kuɗaɗen ya samo asali ne daga umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa haƙƙin ma’aikatan ne, ba wata alfarma da gwamnati ta yi musu ba.

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *