Kamfanin NNPC YA KADDAMAR DA TASHAR MAI TA FARKO MAI TSARIN ZUBA DANKA A ABUJA

FB IMG 1789153406596

Kamfanin NNPC Retail a ranar Alhamis ya kaddamar da tasharsa ta farko mai amfani da fasahar zamani da tsarin kai-da-kai wajen sayen man fetur (self-service), wadda ke kan Bill Clinton Drive, Airport Road, Abuja, lamarin da ke zama wani muhimmin mataki wajen sauya tsarin ayyukan kamfanin na sayar da man fetur.

 

Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da tashar, Mataimakin Shugaban NNPC Ltd. mai kula da bangaren Downstream, Dr. Mumuni Dagazau, ya bayyana tashar a matsayin wata alama ta kudirin NNPC Retail na amfani da sabbin fasahohi wajen samar da saukin amfani, ingantaccen aiki da kyakkyawar hidima ga kwastomomi.

 

Ya yaba wa Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya (NIS) bisa samar da filin da kuma goyon bayan hadin gwiwar da ya taimaka wajen ganin an samar da wannan tashar.

 

Shi ma Manajan Daraktan NNPC Retail, Mr. Huub Stokman, ya bayyana cewa tashar wata shaida ce ta sauyin da ke faruwa a bangaren downstream na masana’antar man fetur a Najeriya, tare da nuna kudirin kamfanin na biyan bukatun masu amfani da man fetur na samun ingantaccen aiki, sauki, sauri da kuma hidima mai inganci.

 

Tashar, wadda ke aiki sa’o’i 24 a rana, tana ba kwastomomi damar zuba man fetur da kansu, inda za su iya kammala hada-hadar saye da kuma zuba ainihin adadin man fetur da suke bukata ba tare da dogaro da ma’aikacin tashar ba.

 

Baya ga haka, tashar na da wuraren cajin motocin lantarki (EV), na’urar wanke motoci ta atomatik, wurin kula da mai da man shafawa, wurin sayar da LPG, da wasu ayyukan jin dadin kwastomomi.

 

Kamfanin ya kuma bayyana cewa yana shirin fadada hanyoyin samar da makamashi a tashar, ciki har da samar da CNG.

 

Kaddamar da tashar na nuna fara wani sabon babi a kokarin NNPC Retail na sauya tashoshin man fetur na gargajiya zuwa cibiyoyin makamashi, sufuri da ayyukan jin dadin jama’a masu amfani da fasahar zamani.

 

Kamfanin ya ce manufar ita ce samar da ingantacciyar hidima wadda za ta fi sauki, sauri da kuma dacewa da bukatun kwastomomi a fadin Najeriya.

FB IMG 1789153431598
Kamfanin NNPC Retail 
FB IMG 1789153426724
Kamfanin NNPC Retail 
FB IMG 1789153434901
Kamfanin NNPC Retail 
FB IMG 1789153415331
Kamfanin NNPC Retail 

Alfijir Labarai — Accurate • Timely • Trusted.

 

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

 

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

 

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

 

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

 

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *