Al’ummar Sumaila da Takai Na Ci Gaba Da Kokawa Kan Lalacewar Hanyoyin Shiga Garuruwansa

IMG 000130 04926 1788476501480

Al’ummar kananan hukumomin Sumaila da Takai na ci gaba da kokawa kan lalacewar hanyar Magami zuwa Tukuda da kuma babbar hanyar Birnin Bako zuwa Takai, duba da yadda hanyar ta ke ci gaba da kara lalacewa

Wani mazaunin yankin ‎Atiku da Saura ya bayyanawa premier Radio cewa hanyar Birnin Bako zuwa Takai babbar hanya ce da mazauna yankin ke amfani da ita wajen futar da amfanin gonarsu da kuma bukatunsu na yau da kullum.

 

Atiku da Saura ya ce hanyar ita ce ta haɗa dukkan ƙauyukan Takai da gari. Haka kuma Ita ce cibiyar kasuwanci da lafiyarsu amma hanyar ta zama taron mutuwa a yanzu.

‎Haka kuma sun bayyana cewa sakamakon rashin hanyar suna tafka asara a gonakinsu na amfanin da suke samarwa

‎Mazauna yankin sun roki Gwaman Kano Abba Kabir Yusuf da Sanatan Kano ta kudu Kawu Sumaila da “yan majalisun su na jiha dana tarayya dasu kawo musu dauki,a daidai lokacin da suke shirin futar da anfanin gonarsu

‎Premeir Radio

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

 

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

 

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

 

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

 

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *