Atiku Abubakar Ya Sake Zunguro Fadar Shugaban Najeriya 

IMG 155405 29826 1788015257122

Editan Jaridar Alfijir Labarai.

…“Yan Najeriya Sunfi Buƙatar A Rage Farashin Man Fetur, Ba Rage Kuɗin Sufuri Ba” Acewar Atiku Abubakar

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa abin da al’ummar Najeriya ke buƙata shi ne a rage musu farashin man fetur, maimakon mayar da hankali kan rage kuɗin sufuri.

Atiku ya ce hauhawar farashin man fetur na daga cikin manyan abubuwan da ke ƙara tsadar rayuwa a ƙasar, musamman sakamakon yadda farashin man ke shafar harkokin sufuri da sauran kayayyaki.

Ya bayyana cewa idan aka samu raguwar farashin man fetur, hakan zai taimaka wajen rage kuɗin sufuri ta hanya mai ɗorewa, tare da sauƙaƙa wa ’yan Najeriya halin matsin tattalin arzikin da suke ciki.

A cewarsa, rage kuɗin sufuri kawai ba zai warware matsalar tsadar rayuwa ba, domin farashin man fetur yana da tasiri kai tsaye kan harkokin kasuwanci da zirga-zirgar jama’a.

Atiku ya kuma yi kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan da za su sauƙaƙa rayuwa ga ’yan Najeriya, musamman ta hanyar samar da makamashi mai rahusa da kuma inganta tattalin arzikin ƙasa.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *