Tsaro: Jami’an Interpol sun ceto mata biyu ‘yan Colombia da aka yi safarar su zuwa Najeriya

FB IMG 1788022918806

Rundunar ‘Yan sandan Najeriya ta hannun hukumar INTERPOL ta ceto mata biyu ‘yan kasar Colombia da ake zargin wata kungiyar masu safarar mutane ta yaudare su tare da tsare su a Najeriya.

 

Kakakin rundunar ‘yansandan kasa, CSP Aniete Iniedu, ya bayyana a ranar Asabar cewa an gudanar da aikin ne bayan samun sahihin bayanan sirri daga ofishin INTERPOL na Bogotá a ranar 26 ga watan Agusta, 2026.

Matan da aka ceto sun hada da Maria Camila Rodas Ortiz da Yuliet Fernanda Rios Mesa.

 

A cewar rundunar, wasu ‘yan kasar China da ake nema ruwa a jallo ne suka yaudari matan zuwa Najeriya, inda suka kwace musu takardun tafiyarsu tare da tsare su ba tare da yardarsu ba.

 

Jami’an INTERPOL na Najeriya sun gudanar da bincike cikin sirri, inda suka gano maboyar da ake tsare da matan a jihar Legas tare da ceto su lafiya.

Sai dai wadanda ake zargin sun tsere bayan sun hango jami’an tsaro suna tunkarar wurin.

 

A halin yanzu, ‘yan sanda sun ce suna ci gaba da kokarin ganowa tare da cafke dukkan mutanen da ke da hannu a wannan harkar.

 

An ajiye matan a wani wuri mai tsaro, yayin da ofishin jakadancin Colombia ke hada kai da hukumomin Najeriya domin tabbatar da komawarsu kasarsu lafiya.

 

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

 

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

 

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

 

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

 

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *