Daga cikin ɗaliban da suka samu Credit a Turanci da Lissafi, 558,883 maza ne, yayin da 641,631 mata ne. Gaba ɗaya, mata 997,267 ne suka rubuta jarabawar, yayin da maza suka kai 953,459.
Hukumar shirya jarabawar ƙasashen yammacin Afirka (WAEC) ta riƙe sakamakon ɗalibai 167,486, daidai da kashi 8.59 cikin 100 na waɗanda suka rubuta jarabawar WASSCE ta kwamfuta (CBT) ta shekarar 2026, sakamakon zargin aikata laifukan satar amsa.
Shugaban ofishin WAEC na Nijeriya, Dokta Amos Dangut, ne ya bayyana hakan yayin sanar da fitar da sakamakon jarabawar a Lagos ranar Laraba.
Ya ce an riƙe sakamakon ne saboda laifuka daban-daban da suka haɗa da amfani da wayoyin hannu a ɗakin jarabawa duk da haramcin da aka yi, da kuma shirya satar amsa a wasu makarantu.
Dokta Dangut ya ce, “Ci gaba da amfani da wayoyin hannu a ɗakin jarabawa duk da dokar hana hakan, da kuma shirya satar amsa a wasu makarantu, na daga cikin manyan matsalolin da muka fuskanta.”
Ya ƙara da cewa an kama wasu masu kula da jarabawa da aka samu suna taimaka wa ɗalibai wajen yin maguɗi, kuma za a miƙa lamarinsu ga ma’aikatun ilimi na jihohi domin ɗaukar matakin ladabtarwa.
A cewarsa, ɗalibai 1,959,668 daga makarantu 24,207 a Nijeriya, Jamhuriyar Benin, Côte d’Ivoire da Equatorial Guinea ne suka yi rajistar jarabawar, yayin da 1,950,726 suka rubuta ta.
Daga cikin waɗanda suka rubuta jarabawar, ɗalibai 1,200,514, daidai da kashi 61.54 cikin 100, sun samu maki na Credit ko sama da haka a aƙalla darussa biyar ciki har da Turanci da Lissafi. Haka kuma, ɗalibai 1,687,378, daidai da kashi 86.50 cikin 100, sun samu Credit a aƙalla darussa biyar ko da ba tare da Turanci da Lissafi ba.
WAEC ta bayyana cewa yawan waɗanda suka samu Credit a darussa biyar ciki har da Turanci da Lissafi ya ragu da kashi 1.42 cikin 100 idan aka kwatanta da sakamakon shekarar 2025.
Daga cikin ɗaliban da suka samu Credit a Turanci da Lissafi, 558,883 maza ne, yayin da 641,631 mata ne. Gaba ɗaya, mata 997,267 ne suka rubuta jarabawar, yayin da maza suka kai 953,459.
Hukumar ta kuma bayyana cewa an kammala tantance sakamakon ɗalibai 1,834,695, daidai da kashi 94.05 cikin 100, kuma an fitar da su, yayin da sakamakon ɗalibai 116,031, daidai da kashi 5.95 cikin 100, ke ci gaba da tantancewa.
Dangut ya ce ɗalibai 1,213 masu buƙata ta musamman sun rubuta jarabawar, ciki har da makafi 137, masu matsalar ji 491, masu larurar motsi da ta kwakwalwa 55, da kuma masu nakasa ta jiki 41.
Ya bayyana cewa jarabawar shekarar 2026 ita ce karo na biyu da WAEC ta gudanar da WASSCE ta kwamfuta ga ɗaliban makarantu.
A cewarsa, hukumar ta ƙaddamar da sabbin tsare-tsare kamar tsarin tantance takardu ta hanyar na’ura (Digital Examiner Mark System), sanya lambobi na musamman a takardun tambayoyi domin rage satar amsa, da kuma sabon tsarin samar da e-PIN kai tsaye domin duba sakamako.
Jarabawar ta gudana tsakanin 24 ga Afrilu zuwa 19 ga Yuni, 2026, inda masu tantance takardu 102,708 suka yi aikin tantancewa a cibiyoyi 88.
Dangut ya kuma sanar da cewa ɗaliban jihohin da gwamnatocinsu ke bin WAEC bashin kuɗin rajista ba za su samu damar ganin sakamakonsu ba har sai an biya dukkan kuɗaɗen da ake bi.
DCL Hausa
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
