Gwamnatin Kano Tare Da Hadin Gwiwar Yan Sanda Sun Kama Wani Likitan Bogi Ya Tara Mutane Da Sunan Rabon Magunguna Marasa Inganci A Panshekara

IMG 012429 05826 1785889479335

Gwamnatin Kano Ta Kama Wani Likitan Bogi Wanda Ya tara daruruwan mutane a Sunan rrabon magunguna Marasa Inganci kuma yana karbe musu yan kudaden su a Panshekara

Ma’aikatar lafiya Æ™arÆ™ashin jagorancin Dr Abubakar Labaran Yusuf da haÉ—in gwiwa da hukumar da take kula da asibitoci masu zaman kansu (PHIMA) , hadi da ma’aikatar dake Dakile duk wasu cututtukan da za su zamo annoba ga al’umma (KNCDC) tare da hukumar Ƴan Sanda ta jihar Kano sun dakile wani rabon tallafi na gangan da gangaci wanda ba bisa ka’ida ba a unguwar Panshekara Kano.

Wani bayanan sirri da waÉ—annan hukumomin suka samu ya tabbatar musu da cewar wani bakon haure ne ya tsallako daga jihar Nassarawa ya sauka a unguwar Panshekara jihar Kano, wanda ya tattara al’umma yana diga musu magunguna a baki da idanunsu ba tare da tantancewa ba.

Hakazalika shi mutumin kuma yana bawa mutane wani koren magani a kalba da sunan wai yana maganin cututtuka guda 100 ba daya, yana karbe kuÉ—in mutane kuma! Al’ummar wannan yankin ne suka sanarwa da hukumar KNCDC da PHIMA wannan danyen aikin nan take waÉ—annan hukumomin suka yi mai yiwuwa sanar da Rundunar Yan’Sanda wajen kamo wannan É—an damfarar tare da kayayyakin magungunan da yake amfani da su.

Wannan na É—aya daga cikin irin nasarorin da gwamnatin jihar Kano take samu a bangarorin lafiya, saboda irin mahimmancin da mai girma gwamna Alh Abba Kabir Yusuf yake bata.

Don haka kwamishinan lafiya ya Æ™ara kira da al’ummar jihar Kano da su Æ™ara saka ido akan duk wani motsin wani ko wasu mutane da basu gamsu da su ba da sunan jami’in lafiya, to lallai a sanar da hukuma mafi kusa.

Ya kara da kira ga masu unguwanni da dagatai kan cewar akwai hanyoyi da hukumar lafiya ta ke bi domin bawa mutane kyautar magunguna, musamman ta ɓangaren hukumar asibitoci ko kuma masarauta ƙarƙashin wakilcin Ɗan Kadan Kano Dr Bashir.

Doka ce kuma haramun ne yin wani gangamin raba magunguna na Bature ko na gargajiya a Kano ba tare da sahalewar ma’aikatar Lafiya ba.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *