Daga Aminu Bala Madobi
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cew da kudin hayar Gidajen sa ne dakuma wasu daga cikin kadarorinsa guda biyu ne a jihar Kaduna yake ciyar da kansa da iyaln sa, inda ya bayyana hakan kan muhimmancin nuna gaskiya da rikon amana a ma’aikatun gwamnati.
A wani taro da jam’iyyar APC ta gudanar a ranar 25 ga watan Janairu a dakin taro na Banquet na fadar shugaban kasa, Buhari ya bayyana ra’ayoyinsa kan kudadensa da harkokin mulki, wanda aka gabatar a cikin harshen Hausa.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa ya mallaki gidaje uku ne kacal: daya a mahaifarsa ta Daura, jihar Katsina, biyu kuma a jihar Kaduna.
Tsohon Shugaban kasar ya bayyana cewa daya daga cikin kadarorin Kaduna wanda ya Bayar da shi hayar, ana amfani da kudin da yake samu wajen biyan bukatunsa na yau da kullum.
Ko menene raayin ku gameda wannan ikirarin tsohon Shugaban kasar?
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp 👇👇
https://chat.whatsapp.com/FNMJaJ3I8Sc0bkkm8aJQbQ
