JERIN BINCIKE: ME AL’UMMAR GWALE SUKA AMFANA DAGA WAKILCIN GARBA DISO?
A ci gaba da jerin rahotanninmu kan ayyukan Hon. Garba Ibrahim Muhammad, wanda aka fi sani da Garba Diso, a Majalisar Wakilai ta Tarayyar Najeriya, wannan fitowa ta mayar da hankali ne kan motions guda biyu da ya gabatar a Majalisa.
Motion na farko ya shafi amfani da fasahar zamani wajen inganta ayyukan Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC), yayin da na biyu ya shafi farfaɗo da masana’antar masaku a Najeriya.
1. MOTION KAN AMFANI DA FASAHA A AYYUKAN FRSC
A ranar 10 ga Oktoba 2024, Garba Diso ya gabatar da motion mai taken “Call on the Federal Road Safety Commission to Adopt Modern Technology in its Operations”.
Motion ɗin ya nemi Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta ƙara amfani da fasahar zamani wajen gudanar da ayyukanta, musamman wajen tabbatar da bin dokokin hanya.
A cikin motion ɗin, an bayyana damuwa kan haɗarin da ka iya tasowa daga wasu shingayen binciken ababen hawa, cunkoson da suke iya haifarwa, zarge-zargen cin hanci a wasu wuraren bincike, da kuma haɗarin bin masu ababen hawa da gudu mai yawa.
Motion ɗin ya ba da shawarar amfani da fasahohi kamar:
1. Automatic Vehicle Location (AVL): Fasahar gano wurin da ababen hawa suke.
2. Automated Traffic Enforcement (ATE): Amfani da na’urori da tsarin fasaha wajen gano laifukan hanya.
3. Advanced Analytics and Data Platforms: Amfani da ingantattun bayanai da nazarinsu domin taimakawa wajen inganta ayyukan hukumar.
Motion ɗin ya kuma nemi FRSC ta riƙa tantance tasirin hanyoyin amfani da fasaha, domin gano ko suna taimakawa wajen rage laifukan hanya da inganta tsaro.
Abin da Majalisa ta yanke:
Takardun zaman Majalisar Wakilai na ranar 10 ga Oktoba 2024 sun nuna cewa an amince da motion ɗin. An kuma umarci Kwamitin Majalisa mai kula da FRSC da ya tabbatar da bin ƙudurin.
2. MOTION KAN FARFAƊO DA MASANA’ANTAR MASAKU A NAJERIYA
A ranar 20 ga Mayu 2025, Garba Diso ya gabatar da motion mai taken “Need to Revamp the Nation’s Comatose Textile Industry”, wato buƙatar farfaɗo da masana’antar masaku ta Najeriya.
A cikin motion ɗin, an bayyana cewa masana’antar masaku ta Najeriya ta taɓa taka muhimmiyar rawa a tattalin arzikin ƙasar, inda aka nuna cewa tana da masana’antun masaku sama da 180 a shekarun 1960 zuwa 1980, tare da samar da ayyukan yi ga kusan ma’aikata 450,000.
An kuma bayyana cewa Najeriya tana da albarkatun ƙasa kamar auduga da ulu waɗanda za su iya taimakawa wajen bunƙasa masana’antar cikin gida.
Sai dai motion ɗin ya nuna damuwa kan koma bayan da masana’antar ta samu a tsawon shekaru, wanda ya jawo rasa ayyukan yi ga dubban ma’aikata a kamfanoni da suka haɗa da Kaduna Textile, Kano Textile, Aba Textile, United Nigeria Textile da First Spinners.
Haka kuma, an ambaci raguwar noman auduga, tsadar samar da kayayyaki, haraji da kuma yawan shigo da masakun ƙasashen waje a matsayin abubuwan da suka shafi ci gaban masana’antar.
SHAWARWARIN DA MOTION ƊIN YA ƘUNSA
Motion ɗin ya ƙunshi shawarwari ga Gwamnatin Tarayya, ciki har da:
1. A daidaita shigo da masakun ƙasashen waje domin ƙarfafa samar da masaku a cikin gida.
2. Ma’aikatar Wutar Lantarki ta Tarayya ta haɗa kai da Ma’aikatar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari wajen samar da abubuwan more rayuwa, musamman wutar lantarki, ga masana’antun masaku.
3. Ma’aikatun da abin ya shafa su ƙarfafa masana’antun cikin gida ta hanyar samar da rance mai sauƙi da damar samun kuɗaɗen jari ta Bank of Industry.
4. Kwamitocin Majalisa masu kula da Masana’antu da Kasuwanci su gudanar da zaman jin ra’ayoyin masu ruwa da tsaki domin nazarin matsalolin masana’antar, tare da gabatar da rahoto cikin makonni huɗu.
GYARAN DA AKA YI KAFIN AMINCEWA DA MOTION ƊIN
A yayin muhawarar motion ɗin, Hon. Osawaru Billy Famous Adesuwa ya gabatar da gyara ga shawarar farko, inda ya nemi a cire kalmar “ban” a saka “regulate”.
Wannan yana nufin cewa, maimakon a hana shigo da masakun ƙasashen waje gaba ɗaya, a daidaita shigo da su domin ƙarfafa samar da masaku a cikin gida.
Takardun Majalisa sun nuna cewa an amince da wannan gyara, sannan aka amince da motion ɗin kamar yadda aka gyara shi.
Abin da Majalisa ta yanke:
Majalisa ta umarci Kwamitocin Industry da Commerce su gudanar da zaman jin ra’ayoyin masu ruwa da tsaki kan matsalolin masana’antar cikin makonni huɗu. Haka kuma, an umarci Kwamitin Legislative Compliance da ya sa ido kan bin ƙudurin.
ABIN DA MOTIONS ƊIN BIYU SUKA ƘUNSA
Motion na FRSC ya mayar da hankali kan amfani da fasahar zamani wajen inganta aikin kiyaye hanya, yayin da motion na masana’antar masaku ya shafi farfaɗo da masana’antu, samar da ayyukan yi da ƙarfafa tattalin arzikin cikin gida.
Dukansu sun shafi batutuwan da suka shafi ƙasa baki ɗaya, kuma suna cikin ayyukan majalisa da Garba Diso ya gabatar a matsayinsa na ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Gwale.
KAMMALAWA
Takardun Majalisar Wakilai sun tabbatar da cewa Garba Diso ya gabatar da waɗannan motions guda biyu, kuma Majalisar ta amince da su.
Motion na farko ya shafi amfani da fasaha a ayyukan FRSC, yayin da na biyu ya shafi farfaɗo da masana’antar masaku ta Najeriya.
Wannan fitowa ta gabatar da abubuwan da motions ɗin suka ƙunsa da matakan da Majalisa ta ɗauka, ba tare da ɗauka cewa an riga an aiwatar da dukkan shawarwarin ba.
A ci gaba da wannan bincike, Alfijir Labarai na gabatar da ayyukan da Garba Diso ya bayyana, tare da amfani da takardun hukuma domin taimaka wa al’ummar Gwale su fahimci ayyukan wakilcinsu.
—
MADOGARAR RAHOTO
1. House of Representatives, Votes and Proceedings, Thursday, 10 October 2024:
https://placng.org/i/wp-content/uploads/2025/06/House-of-Reps-votes-and-proceedings-Thursday-10-October-2024.pdf
2. House of Representatives, Votes and Proceedings, Tuesday, 20 May 2025:
https://placng.org/i/wp-content/uploads/2025/06/House-of-Reps-votes-and-proceedings-Tuesday-20-May-2025.pdf
📢 FOLLOW ALFIJIR LABARAI
Stay connected with Alfijir Labarai / Alfijir News for credible news, reports, investigative journalism, and important updates from Kano, Nigeria, and around the world.
📩 CONTACT US & PARTNERSHIP ENQUIRIES
Call/WhatsApp: +234 701 1 11 3809
+234 803 207 7835
🌐 OUR SOCIAL MEDIA PLATFORMS
X: https://twitter.com/Musabestseller?s=09
Facebook: https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
Threads: https://www.threads.net/@alfijirlabarai
YouTube: https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Instagram: https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
📲 JOIN OUR WHATSAPP GROUP
https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f
ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES
Truth • Timeliness • Trust
© 2026 Alfijir Labarai Media Services
