Gwamna Adeleke Ya Ja Hankalin Tinubu Kan Barazanar Janye Tsaro A Cibiyoyin Tattara Sakamakon Zaben Osun

IMG 20260815 WA1935

Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya gargadi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan wasu barazanar tsaro da ake zargin za su iya shafar cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe a jihar.

Adeleke ya bayyana damuwarsa kan rahotannin da ke cewa akwai wani shiri da zai iya janyo matsalar tsaro a wuraren da za a gudanar da tattara sakamakon zaɓen.

Gwamnan ya kuma yi zargin cewa ana shirin janye jami’an tsaro daga wasu muhimman wurare a lokacin da ake bukatar cikakken tsaro, yana mai cewa hakan na iya haifar da barazana ga zaman lafiya da tsarin zaɓe.

Adeleke ya yi kira ga Shugaba Tinubu da hukumomin tsaro da su dauki matakin gaggawa domin tabbatar da tsaro a cibiyoyin tattara sakamako, tare da kare tsarin dimokuraɗiyya da tabbatar da cewa jama’a sun samu damar gudanar da harkokin zaɓe cikin lumana.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *