Rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya Ya Nuna Ana Samun Karancin Maza A Duniya.

IMG 20260815 WA1936

Wani rahoton da Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ya yi ikirarin cewa ana samun ƙarancin maza a duniya, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta.

Rahoton ya ce a cikin mutane biliyan 7.8 da ake da su a duniya, mata sun kai kimanin biliyan 5.6, yayin da maza suka kai biliyan 2.2. Sai dai ba dukkan mazan ne ake ganin suna cikin yanayin neman aure ba.

A cewar rahoton, daga cikin mazan biliyan 2.2, wasu kusan biliyan ɗaya sun riga sun yi aure, yayin da wasu ke gidan yari ko kuma fama da matsalolin lafiya daban-daban.

Rahoton ya kuma yi ikirarin cewa daga cikin mazan da ake ganin suna samuwa domin aure, akwai masu aikin yi ko rashin aikin yi, manya da suka tsufa, limaman addini da kuma wasu da ke da wasu dalilai da za su iya hana su shiga aure.

Kan wannan kididdiga, da aka danganta da wannan rahoton ya yi kira ga mata da su rika girmama da kyautata mu’amala da maza, yana mai cewa akwai ƙarancin maza a wasu sassan duniya. Sai dai ana cigaba da sabunta alkaluma la’akari da yadda abubuwa ke iya canzawa a ko da yaushe

Menene Ra’ayin Ku?

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

 

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

 

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

 

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

 

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *