Gwamnan Kano ya lashe babbar Kyautar Jagoranci ta ƙasa da ƙasa wajen sauya fasalin ilimi a jihar daga London

IMG 20260725 WA1951

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya samu babbar Kyautar Jagoranci ta Ƙasa da Ƙasa a Fannin Ilimi da Inganta Karatu (International Literacy and Learning Leadership Award), domin karrama jajircewarsa da kuma ingantaccen jagoranci wajen sauya fasalin harkokin ilimi a Jihar Kano baki ɗaya.

An baiwa Gwamna Abba kyautar ne ta hannun Universal Learning Solutions (ULS) a wani biki na musamman da aka gudanar a Stationers’ Hall mai tarihi, da ke birnin Landan na Birtaniya, a matsayin wani ɓangare na bukukuwan cika shekaru 20 da fara shirin Jolly Phonics a nahiyar Afirka.

Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II, ne ya karɓi kyautar a madadin Gwamna Yusuf, wadda masu shirya taron suka ce sun bashi ne saboda kudin da gwamnatinsa ta zuba a fannin ilimi, musamman matakin ware kashi 30 cikin 100 na kasafin kuɗin Jihar Kano ga ilimi, wanda ke cikin mafi girman kaso da aka ware wa ilimi a Najeriya.

Alfijir labarai na taya mai girma gwamna Abba Kabir Yusuf murnar lashe wannan babbar kyauta mai mahimmanci kwarai da gaske a gareshi da al’ummar jihar Kano baki ɗaya.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *