Cikin Hirarsa da BBC ministan yaɗa labaran ƙasar, Mohammed Idris ya ce Najeriya ba ta taɓa ƙulla wata alaƙar soji da Faransa ko wata ƙasa domin ɗaukar nauyin hare-haren ta’addanci a Jamhuriyar ta Nijar, ko tayar da zaune-tsaye a ƙasar.
Mohammed Idris ya ce shugaban Najerya Bola Tinubu a matsayinsa na shugaban Ecowas yana gudanar da jagoranci da ya kira ‘abin koyi’.
”Kuma Najeriya na iya bakin ƙoƙarinta wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma tabbatar da ɗorewar danganta mai tarihi tsakaninta da Jamhuriyar Nijar”, in ji Ministan.
Ministan yaɗa labaran na Najeriya ya ce dakarun ƙasar, tare da haɗin gwiwar dakarun ƙasashen da ke yaƙi a Tafkin Chadi na samun nasara a yaƙin da suke yi da ‘yanta’adda a yankin.
”Don haka wani ya yi zargin cewa Najeriya za ta haɗa baki da wata ƙasar waje domin wargaza zaman lafiya da tsaron makwabciyarta” ba gaskiya bane, in ji Mohammed Idris.
Dangane da zargin wasu jami’an gwamnatin Najeriya da Janar Tchiani na cewa suna ɗaukar nauyin ‘yan tadda da ba su horo kuwa, ministan yaɗa labaran ƙasar ya ce babu ƙamshin gaskiya game da zargin.
”Gwamnatin Najeriya ko wani jami’inta ba su taɓa sanya hannu a bai wa ‘yan ta’adda tallafin makamai domin kai wa Nijar hari”, in ji shi.
Haka kuma ministan ya musanta zargin bai wa Faransa wuri domin kafa sansani. ‘‘Najeriya ba ta taɓa bai wa wata ƙasar waje damar kafa sansanin soji ba.
‘Zarge-zarge ne marasa tushe cewar ” Ministan yaɗa labaran Najeriya”
Haka kuma ministan ya musanta zargin da shugaban na Nijar ya yi wa Najeriya na yi wa bututun manta da harkokin noman ƙasar zagon-ƙasa.
Mohammad Idris ya ce Najeriya ta riƙa gudanar da abubuwa na tallafa wa tattalin arzikin Nijar ta hanyar shirye-shiryen samar da makamashi, kamar shimfiɗa bututu iskar gas, na ‘Trans-Saharan Gas Pipeline’ da shimfiɗa layin dogo daga Kano zuwa Maraɗi.
”Babu hikima mutum ya yi tunanin cewa Najeriya na yi abin da zai durƙusar da tattalin arzikin Nijar”.
Kan batun zargin hadin bakin Najeriya da Faransa wajen kafa cibiyar Lakurawa a jihar Sokoto, ministan ya ce zargi ne maras tushe.
”Najeriya ta kasance ja gaba a yaƙi da ta’addanci, inda take sadaukar da kuɗaɗe masu yawa da rayukan jami’anta domin tabbatar da zaman lafiya a yankin Tafkin Chadi”, in ji Mohammed Idris.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj
