Hankali Shi Yake Gani: Dawo da tallafin man fetur zai mayar da tattalin arzikin Najeriya baya – In Ji Minista

FB IMG 1787582792149

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed IdrisAsalin hoton,Mohammed Idris/X

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya ce idan aka dawo da tallafin man fetur zai mayar da tattalin arzikin Najeriya baya cikin matsalolin da ta fuskanta a shekarun baya.

A wata sanarwa ma’aikatar ta wallafa a shafinta na sada zumunta a ranar Litinin, ministan ya ce cire tallafin ya samar wa gwamnati da ƙarin damar kashe kuɗi a fannoni kamar ilimi, lafiya, ababen more rayuwa da tsaro.

Ya kara da cewar dawo da tallafin zai sake jefa ƙasar cikin matsi wajen yin kasafin kuɗi da ƙara wa gwamnati wani nauyi a kan kuɗaɗen da take da su.

Ministan ya ce masu son a dawo da tallafin ya kamata su yi la’akari da abin da ƙasar za ta rasa wajen gudanar da wasu shirye-shiryen, inda ya ce tun bayan cire tallafin, gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi sun samu ƙarin kuɗaɗen da suka kai kusan naira tiriliyan 15.8 tsakanin Yunin 2023 zuwa Disamban 2025.

Ya ce an kashe kusan naira tiriliyan 6.47 kan manyan ayyukan more rayuwa, yayin da sama da naira biliyan 400 aka ware wa wasu shirye-shiryen tallafawa jama’a, ciki har da NELFUND, asusun saka hannun jari a gidaje da kuma shirye-shiryen rance ga ‘yan ƙasa da ‘yan kasuwa.

“Shin mu dawo da tallafin man fetur, ko mu ci gaba da tallafawa shirin lamunin karatu ga matasan Najeriya?” in ji ministan

Ya kuma tambayi masu suka tsarin “ko a dawo da tallafin ne maimakon ci gaba da ba jihohi da ƙananan hukumomi ƙarin kuɗaɗen shiga, da kuma ci gaba da samun kuɗin gina hanyoyi, layin dogo, wutar lantarki da tsaro?”

Ministan ya yi kira ga ƴan Najeriya da su duba sauye-sauyen tattalin arzikin da za a ci gajiyar shi na dogon lokaci, yana mai cewa manufar ita ce gina tattalin arziki mai ƙarfi da zai iya samar da ci gaba mai ɗorewa.

BBC

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *