HISBAH TA KANO TA GURFANAR DA ’YAN TIKTOK MATA UKU A KOTU KAN ZARGIN BIDIOYIN DA SUKA SAƁA WA TARBIYYA

IMG 232628 241026 1792880797476

HISBAH

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta cafke wasu mata uku, ciki har da ’yar TikTok mai suna Amani Ishaq, bisa zargin yaɗa bidiyoyin da ake zargin sun saɓa wa tarbiyya a shafukan sada zumunta.

Bayanin da Mataimakin Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Dr. Mujahid Aminuddeen, ya fitar ya bayyana cewa an gurfanar da matan ukun a gaban Kotun Majistare mai lamba biyar da ke Court Road, Kano.

Matan da aka gurfanar su ne Hauwa Khamis, Sa’adatu Muhammad da Amani Ishaq.

Sanarwar ta ce ana zargin Amani Ishaq da yaɗa wasu bidiyoyin rawa a dandalin TikTok waɗanda ake zargin sun ƙunshi abubuwan da suka saɓa wa tarbiyya da koyarwar addinin Musulunci.

Sai dai waɗannan zarge-zarge ne da aka gabatar a gaban kotu; ba za a ɗauke su a matsayin tabbataccen laifi ba har sai an kammala shari’a kuma kotu ta yanke hukunci.

ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES

📢 KU BI ALFIJIR LABARAI

Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sahihan labarai, rahotanni, bincike da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da duniya.

📩 TUNTUƁA DA HAƊIN GWIWA
Kira/WhatsApp: +234 803 207 7835

🌐 KAFAFEFENMU
X: https://twitter.com/Musabestseller?s=09
Facebook: https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
Threads: https://www.threads.net/@alfijirlabarai
YouTube: https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Instagram: https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

📲 WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f

ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES
Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce

© 2026 Alfijir Labarai Media Services

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *