Hukumar NSCDC Ta Hukunta Jami’anta 79 Kan Laifukan Rashin Da’a da Sabawa Dokokin Aiki 

FB IMG 1786017998346

Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) ta ɗauki matakan ladabtarwa kan jami’anta 79 saboda saɓa wa ƙa’idojin aiki, inda wasu suka haɗa da kora daga aiki, ritaya dole da kuma ba da shawarar gurfanar da wasu a gaban kotu.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar ta ƙasa, Babawale Afolabi, ya fitar.

Sanarwar ta bayyana cewa an kammala binciken ladabtarwa kan jami’ai 75 da ake zargi da laifuka daban-daban, ciki har da damfarar aikin yi, rashin gaskiya a harkokin kuɗi, sata, rashin zuwa aiki ba tare da izini ba da kuma aikata abubuwan da suka saɓa wa tsaron ƙasa.

Ta ƙara da cewa an kori jami’ai biyu kan lamarin da ya yi sanadin mutuwar Kwamandan Mining Marshals, Levi Agada, a Rafin Gabas da ke Ƙaramar Hukumar Kokona ta Jihar Nasarawa a ranar 18 ga Fabrairu, 2026. Hukumar ta ce jami’an sun yi amfani da bindiga ba tare da izini ba yayin wani aiki da ya shafi masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, tare da ba da shawarar a gurfanar da su a kotu.

Hukumar ta kuma bayyana cewa jami’ai huɗu na ci gaba da fuskantar binciken ladabtarwa kan zargin safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba, yayin da ake gudanar da bincike kan wasu mutane da ake zargi da lalata muhimman kayayyakin gwamnati da kuma safarar makamai.

Ta jaddada cewa duk waɗanda abin ya shafa suna da haƙƙin samun adalci kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *