“Idan Na Lashe Zaɓe, Zan Buɗe Boda, Kowa Ya Warwasa” – Atiku Abubakar

IMG 20260828 WA0403

Daga Aminu Bala Madobi

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana wani shiri da yake cewa zai aiwatar idan har ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa.

Atiku ya ce daga cikin matakan da zai ɗauka shi ne buɗe iyakokin Najeriya, wato cire wasu takunkumin da ake zargin suna hana zirga-zirgar kaya da mutane cikin sauƙi tsakanin Najeriya da ƙasashen maƙwabta.

Ya bayyana cewa buɗe iyakokin na iya taimakawa wajen bunƙasa harkokin kasuwanci, ƙara zirga-zirgar kayayyaki da kuma samar da damarmaki ga ’yan kasuwa da sauran masu sana’o’i.

Sai dai batun buɗe iyakokin na iya haifar da muhawara, musamman kan tsaro, fasa-ƙwauri da kuma yadda hakan zai shafi masana’antun cikin gida.

Atiku ya ce manufarsa ita ce ganin an samar da tsarin da zai amfani tattalin arzikin ƙasa da kuma jama’a.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

 

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

 

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

 

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

 

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *