INEC ta ayyana Charles Soludo na APGA a matsayin wanda ya lashe zaɓen Gwamnan Anambra
Charles Soludo dai ya kasance tsohon gwamnan Babban Bankin Nijeriya CBN daga 2004 zuwa 2009.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana Charles Chukwuma Soludo na Jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna da aka gudanar a ranar 8 ga Nuwamba a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Nijeriya.
Farfesa Edoma Omoregie, wanda shi ne babban baturen zaɓe na jihar ne ya sanar da sakamakon a cibiyar tattara sakamakon ta INEC da ke Awka, babban birnin jihar, da safiyar Lahadi.
A cewar sakamakon, Soludo ya samu ƙuri’u 422,664, yayin da Nicholas Ukachukwu na Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya biyo baya da ƙuri’u 99,445.
Paul Chukwuma na Jam’iyyar Young Progressives Party (YPP) ne ya zo na uku a zaɓen da ƙuri’u 37,753.
George Moghalu na Jam’iyyar Labour Party (LP) ne ya zo na huɗu da ƙuri’u 10,576, yayin da Jude Ezenwafor na Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya samu ƙuri’u 1,401.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
