Amurka ta yi amfani da “kusan dukkan” waɗannan makamai, a cewar rahoton kamfanin dillacin labarai na Reuters, tana ambaton majiyoyi da suke da masaniya kan lamarin.
Rundunar Sojin Amurka ta yi amfani da mafi yawan makamai masu linzaminta da ke cin dogon zango a lokacin yakin watanni biyar da ta shafe tana yaƙi da Iran, a cewar wani rahoto.
Kuma galibi tsarin makamai masu linzamin na rundunar sojin sama da ƙasa ne, waɗanda aka fi sani da Army Tactical Missile Systems (ATACMS) da Precision Strike Missiles (PrSM).
Amurka ta yi amfani da “kusan dukkan” waɗannan makamai, a cewar rahoton kamfanin dillacin labarai na Reuters, tana ambaton majiyoyi da suke da masaniya kan lamarin.
A baya dai, ba a samu rahotanni kan yadda sojojin ke fuskantar ƙarancin makamai na ATACMS da Precision Strike Missiles ba.
Farashin kowanne makami mai linzami da ke cin dogon zango ya kai fiye da dala miliyan 1, kuma yana daga cikin wani muhimmin ɓangare na makaman sojojin, wanda ke ba da damar kai hari daidai saiti kuma daga nesa.
Makaman ATACMS da Amurka ke samarwa sun taka muhimmiyar rawa a yakin Ukraine, wanda ya ba sojojin Ukraine damar kai hari kan wurare da dama a Rasha.
PrSM wani sabon samfurin ci gaban makami mai linzami wanda zai maye gurbin ATACMS, da ke cin gajerar zango.
Ƙarancin makamai masu linzami da ke cin dogon zango, na nufin shugaban Amurka Donald Trump zai koma dogaro kan harba bama-bamai masu haɗari idan ya sake ƙaddamar da manyan hare-hare kan Iran.
Rashin samar da makamai masu linzami na iya rage ikon Amurka kan abokan gabanta, ciki har da Rasha da China.
Rundunar CENTCOM ta Amurka ta ruwaito amfani da kusan dukka makamai masu linzami na ƙasa da take da su kafin soma yaƙin; ta samu damar sake samun wasu makaman daga sojojin Amurka a wasu yankuna a duniya.
Fadar White House ta ce Amurka tana da “makamai masu yawa fiye da kowa a duniya” kuma “fiye da abin da muke buƙata.”
“Kamfanonin tsaronmu, a yanzu, suna samar da makamai masu yawa fiye da yadda suke yi a baya, baya ga faɗaɗa masana’antunsu da kayan aikinsu zuwa wasu matakai,” in ji Trump.
TRT Afrika Hausa.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
