KOTU TA TSARE ‘YAR TIKTOK YAR LELE KAN ZARGIN ƁATA SUNA

IMG 165101 19926 1789833071217

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Post Office, Kano, ta bayar da umarnin tsare Khadija Muhammad, wadda aka fi sani da “Yar Lele”, a gidan gyaran hali kan zargin ɓata suna da cin zarafi.

 

Wakilin Freedom Radio, Aminu Abdu Bakanoma, ya ruwaito cewa ’yan sanda ne suka gurfanar da Khadija a gaban kotun da Alƙali Garba Malafa ke jagoranta.

 

Bayan an karanta mata tuhume-tuhumen da ake zarginta da su, Khadija ta musanta aikata laifukan.

 

Mai gabatar da ƙara, Barista Awaisu Sani Lawan, ya buƙaci kotun ta ba su lokaci domin gabatar da shaidu da sauran bayanan da za su taimaka wajen gabatar da ƙarar.

 

Bayan sauraron ɓangarorin, kotun ta ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 14 ga Oktoba, 2026.

 

Ana zargin Khadija da wallafa wani bidiyo da ake cewa yana ɗauke da kalaman da suka shafi mutuncin MD Hassan, wani ɗan siyasa a Ƙaramar Hukumar Nassarawa ta Jihar Kano.

 

Sai dai zarge-zargen ba su zama tabbatattun laifuka ba, domin kotu ba ta yanke hukunci kan lamarin ba. Khadija kuma ta musanta tuhume-tuhumen da ake mata.

 

Alfijir Labarai za ta ci gaba da bibiyar shari’ar tare da kawo muku sabbin bayanai yayin da ake samun su.

 

📢 KU CI GABA DA BIN ALFIJIR LABARAI

 

Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sabbin labarai, rahotanni, bincike, shirye-shirye da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

 

📞 TUNTUBE MU

 

Domin samun ƙarin bayani, turo mana da labari, haɗin gwiwa, tallace-tallace, ɗaukar nauyin shirye-shirye ko wasu buƙatu:

 

📱 +234 803 207 7835

 

📰 Kuna da labari ko wani muhimmin bayani?

Ku turo mana da labaran gaggawa, sanarwar hukumomi, jawabi, sanarwar taro da abubuwan da suka shafi al’umma domin tantancewa da yaɗawa.

 

🤝 KU YI HAƊIN GWIWA DA MU

 

Muna maraba da mutane, ƙungiyoyi, hukumomi da ‘yan kasuwa masu sha’awar:

 

• Haɗin gwiwar kafafen yaɗa labarai

• Tallace-tallace

• Daukar nauyin shirye-shirye

• Haɗin gwiwar kamfanoni da hukumomi

• Rahotanni na musamman da bincike

• Tallata taruka da shirye-shirye

 

📞 Domin tattaunawa:

+234 803 207 7835

 

🌐 KU BI MU A KAFAFEN SADA ZUMUNTA

 

🐦 X (Twitter):

 

“Ku bi mu a X” https://twitter.com/Musabestseller?s=09

 

📘 Facebook:

 

“Ku bi mu a Facebook” https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

🧵 Threads:

 

“Ku bi mu a Threads” https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

▶️ YouTube:

 

“Ku yi Subscibe a YouTube https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

📸 Instagram:

 

“Ku bi mu a Instagram” https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

📲 SHIGA GROUP WHATSAPP

 

Ku kasance cikin masu samun sabbin labarai, shirye-shirye, rahotanni da muhimman sanarwa kai tsaye ta WhatsApp.

 

👇👇

https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f?s=cl&p=a&mlu=4&ilr=4

 

ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES

 

Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce

 

📰 Labarai • Rahotanni • Bincike • Shirye-shirye • Wayar da Kai

 

© 2026 Alfijir Labarai Media Services

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *