Majalisar dokokin jihar Jigawa ta amince da kudurin kasafin kudi na shekarar 2025 na sama da naira biliyan 698 na ayyukan gwamnatin jihar da kuma naira biliyan 184 na ayyukan kananan hukumomi 27.
Hakan ya biyo bayan gabatarwa da kuma amincewa da rahoton kwamitin kasafin kudi na majalisar.
Da yake gabatar da rahotan shugaban kwamatin wanda shi ne mamba mai wakiltar mazabar Malam Madori, Alhaji Hamza Adamu Ibrahim ya bayyana cewa dukkanin kwamitocin majalisar sun tantance tanade-tanaden kasafin kowace ma’aikatar da hukumomi domin yiyuwar gyara ko kari a cikin kasafin kudin.
A cewarsa, kwamitocin sun kuma yi da masu ruwa da tsaki daban-daban da suka hada da kungiyoyin farar hula tare da gudanar da aikin tantancewa a kokarin da ake na isa ga wani cikakken kasafin kudi domin gabatar da shi ga zaman majalisar.
Bayan amincewar baki daya ta hanyar kada kuri’a, shugaban majalisar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya sanar da amincewa da kudurin kasafin kudin shekarar 2025 ya zama doka.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj