Majalisar Dokokin Jihar Kano ta buƙaci a sake duba dokar kula da haya a jihar, sakamakon hauhawar kuɗin hayar gidaje da shaguna, wanda ke ƙara jefa mazauna jihar da ƙananan ’yan kasuwa cikin matsin tattalin arziki.
Kakakin Majalisar, Isma’il Falgore, ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar ranar Talata, bayan ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Takai, Musa Kachako, ya gabatar da ƙuduri kan matsalar hauhawar kuɗin haya.
A yayin gabatar da ƙudurinsa, Kachako ya bayyana cewa kuɗin hayar wasu gidaje da a baya ake biya naira 100,000 a shekara ya tashi zuwa tsakanin naira 200,000 da 300,000. Haka kuma, ya ce hayar wasu shaguna ta ƙaru daga naira miliyan ɗaya zuwa miliyan biyu cikin shekara guda.
Ɗan majalisar ya kuma nuna damuwa kan yadda wasu masu gidaje ke ƙara kuɗin haya ba tare da bai wa ’yan haya isasshen sanarwa ba, lamarin da ya ce yana ƙara wa ’yan kasuwa, manoma da masu ƙaramin ƙarfi wahalar rayuwa.
Kachako ya jaddada cewa duk da haƙƙin masu gidaje na samun ribar jarin da suka zuba, ya kamata a samar da ƙa’idojin da za su tabbatar da adalci, isasshen lokacin sanarwa da kuma hana ƙarin kuɗin haya fiye da kima.
Ya bayyana cewa sake duba dokar zai taimaka wajen fayyace yadda ya kamata a riƙa ƙara kuɗin haya, tare da daidaita haƙƙoƙin masu gidaje da na ’yan haya.
Majalisar na sa ran cewa sake duba dokar zai taimaka wajen magance matsalolin da ke tattare da hauhawar kuɗin haya da kuma inganta dangantaka tsakanin masu gidaje da masu haya a jihar.
Sai dai, matakin da za a ɗauka kan dokar da kuma lokacin da za a fara aiwatar da duk wani sauyi za su buƙaci ƙarin bayani daga majalisar.
ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES
Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce
📩 Tuntuɓa da haɗin gwiwa: +234 803 207 7835
🌐 X: https://twitter.com/Musabestseller?s=09
Facebook: https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
Threads: https://www.threads.net/@alfijirlabarai
YouTube: https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Instagram: https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
📲 WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f
© 2026 Alfijir Labarai Media Services
