Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da amincewa da kamfanonin jiragen sama guda biyar da za su gudanar da jigilar mahajjatan Najeriya a aikin Hajjin shekarar 2027.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Alhamis, ta bayyana kamfanonin da aka amince da su da suka hada da Air Peace Limited, Flynas, Max Air Limited, Saudi Air da UMZA Aviation Services Limited.
NAHCON ta ce an zabi kamfanonin ne bayan wani cikakken tantancewa da kwamitin tantance kamfanonin jiragen sama ya gudanar, bisa la’akari da ka’idojin tsaro, karfin gudanar da aiki da kuma yanayin harkokin kudi.
Hukumar ta bayyana cewa amincewar ta dogara ne da kammala yarjejeniyar jigilar maniyyata da NAHCON, tare da cika dukkan sharuddan Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya da kuma Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Saudiyya na aikin Hajjin 2027.
Ta kara da cewa za a tsara rabon maniyyata da jadawalin zirga-zirgar jiragen sama tare da hukumomin jin dadin alhazai na jihohi da kuma kamfanonin jiragen da abin ya shafa.
Hukumar ta kuma gargadi kamfanonin da aka amince da su da su tabbatar da bin ka’idojin aikin Hajjin 2027, ciki har da bayar da tikitin jirgi da ke da alaka da bayanan maniyyata na Nusuk-Masar, da kuma kiyaye dukkan ka’idojin tsaro.
NAHCON ta kuma ce dole ne kowane mahajjaci ya samu damar daukar akwati guda mai nauyin kilogram 32 da kayan hannu mai nauyin kilogram 8, kamar yadda hukumomin kula da harkokin jiragen sama suka tanada.
A karshe, hukumar ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su hada kai da kamfanonin da aka amince da su, domin tabbatar da jigilar maniyyatan Najeriya cikin sauki, tsaro da kuma jin dadi.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
