Nan ba da jimawa ba; Ganduje da wasu za su balle daga APC zuwa PDP – Inji Sule Lamido

IMG 20250511 WA0449

Daga Aminu Bala Madobi

Jigo a jam’iyyar PDP, kuma tsohon ministan harkokin waje, Alhaji Sule Lamido, ya ce akwai alamun cewa nan ba da dadewa ba jam’iyyar APC za ta iya rabuwa, inda shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Ganduje da sauran su, zasu koma PDP.

Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a babban taron jam’iyyar PDP da aka gudanar a Aminu Kano Triangle dake Dutse a Jigawa.

Ya ce, “Ina da yakinin cewa duk wadanda suka bar PDP za su dawo ciki har da Ganduje, domin nan ba da dadewa ba APC za ta balle, ta rabu gida biyu, inda PDP zata karbi mutane masu fikira da tunani daban-daban.

“Na fada na mimaita, kuma ina sake maimaitawa: nan da watanni shida, duk wadanda suka koma APC za su dawo, kuma PDP za ta tashi da karfi don kwace mulki a 2027.”

Tsohon ministan harkokin wajen kasar ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar da kada su karaya saboda sauya sheka da wasu zababbun shugabannin sukeyi bayan cin zabe karkashin jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki, yana mai alakanta abin da suka yi da fargaba da ke cigaba da mamaye su.

Wannan kalamai da Lamido ya yi wa jam’iyyar APC na zuwa ne a daidai lokacin da fargaba ke cigaba da hauhawa bayan wasu zababbun yan siyasa ke t sauya sheka daga jam’iyyun adawa zuwa jam’iyya mai mulki.

Ya kuma jaddada cewa jam’iyyar PDP na da kwarin gwiwa da karfin gwiwa na iya kayar da abokan hamayyarta a zaben 2027.

Kalaman Lamido sun kuma tabo batutuwan da suka shafi shugabanci da yadda ake gabatar da shugabancin mulki a Najeriya, wadanda yake ganin jam’iyyar APC ce ke zagon kasa.

“Najeriya kasa ce albarka, amma a kullum shugabanni ne matsalar,” inji shi.

Don haka ya gargadi gwamnatin da ke kan karagar mulki da ta daina tursasa ‘yan adawa, yana mai cewa irin wannan abu na iya haifar da rashin kwanciyar hankali da rarrabuwar kai tsakanin yan kasa.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *