NOMA TUSHEN ARZIKI
Mu Bincika. Mu Tambaya. Mu Bayyana Abubuwan da Muka Gano: Daga Alfijir Labarai
Bincike na Musamman daga Alfijir Labarai
Talata, 29 ga Satumba 2026
DAGA TALLAFIN GONA ZUWA GA MANOMI:
ME YA SAUƘA ZUWA ƘASA A KANO?
Gabatarwa
A makon da ya gabata, Alfijir Labarai ya binciki kasafin kuɗin noma na Jihar Kano na shekarar 2026, tare da duba yadda aka tsara kashe kuɗaɗen da aka ware wa fannin.
Bincikenmu ya nuna cewa an ware kusan ₦26.47 biliyan ga fannin Agriculture, yayin da rahoton Q2 2026 ya nuna aiwatar da kusan ₦13.56 biliyan zuwa ƙarshen Yuni. Ma’aikatar Tsare-tsare da Kasafin Kuɗi ta Kano ce ta wallafa rahoton Q2.
A wannan makon, bincikenmu ya matsa kusa da matakin manomi.
Ba za mu tsaya kan abin da aka ware ko abin da gwamnati ta sanar ba.
Za mu duba wasu daga cikin shirye-shiryen tallafin noma da aka fara aiwatarwa, musamman taki da ban-ruwa, sannan mu bambanta tsakanin abin da aka sanar, abin da aka fara rabawa da abin da za mu iya tabbatar da cewa ya isa ga manomi.
1. TAKI 90,000: AN ƘADDAMAR DA RABON
A watan Yulin 2026, Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon buhunan taki 90,000 ga manoma a faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Channels Television ta ruwaito cewa shirin ya shafi 848 political wards, yayin da Voice of Nigeria ta bayar da adadin 484 wards. Wannan bambancin ya sa Alfijir Labarai ba zai ɗauki ɗaya daga cikin adadin a matsayin tabbataccen adadi ba tare da ƙarin takardar hukuma da ta fayyace batun ba.
Gwamnatin Kano ta bayyana cewa za a sayar da buhun takin ga manomi a ₦25,000, yayin da ta bayyana farashin kasuwa da kusan ₦50,000.
Saboda haka, abin da bincikenmu zai fi mayar da hankali a kai shi ne yadda rabon ya gudana a zahiri da kuma yawan manoman da suka samu.
2. TALLAFIN TARAYYA MA YA SHAFI KANO
Bincikenmu ya kuma gano wani shirin Gwamnatin Tarayya ta National Agricultural Development Fund, NADF.
A watan Yunin 2026, NADF ta ƙaddamar da rabon buhunan taki 100,800 ga ƙananan manoma 25,200 a jihohin Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi da Jigawa.
A tsarin shirin, kowace jiha da ke cikin wannan rukunin za ta samu buhuna 20,160 domin rarrabawa manoma 5,040, yayin da kowane beneficiary zai samu buhuna huɗu na taki kyauta.
Wannan yana nuna cewa akwai shirye-shiryen tallafin taki daga matakin jiha da kuma na tarayya.
Amma a aikin bincike, dole ne a raba waɗannan shirye-shirye domin a san tushen tallafin da kuma waɗanda suka amfana.
3. BAN-RUWA: FASAHAR SOLAR TA SHIGO
A ranar 2 ga Satumba 2026, National Agency for Science and Engineering Infrastructure, NASENI, ta gudanar da demonstration na tsarin solar-powered irrigation a Kano.
Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a ta Tarayya ta ce an gudanar da demonstration ɗin a Fadamar Ruwan Tsamiya irrigation site a Zakirai, Gabasawa, da Tudun Kaba kusa da kogi a Kumbotso.
Shirin yana gudana ne tare da haɗin gwiwar International Water Management Institute, IWMI.
Manufar fasahar ita ce rage dogaro da famfunan ruwa masu amfani da fetur ko dizal, wanda zai iya rage kuɗin noman rani.
Amma ya kamata a fayyace cewa bayanan da muka samu suna magana ne kan demonstration a wasu wurare; ba hujjar cewa tsarin ya riga ya isa ga manoman Kano baki ɗaya ba.
4. ME BAYANANMU SUKA TABBATAR ZUWA YANZU?
Abubuwan da muka samu sun tabbatar da cewa:
An ware kuɗaɗe masu yawa ga fannin noma a kasafin Kano na 2026, kuma rahoton Q2 ya nuna aiwatar da wani babban ɓangare na kasafin zuwa ƙarshen Yuni.
An ƙaddamar da rabon buhunan taki 90,000 a Kano.
Akwai kuma shirin NADF na tallafin taki ga ƙananan manoma, wanda Kano na cikin jihohin da suka shiga.
An kuma gabatar da tsarin solar irrigation a wasu wurare na Gabasawa da Kumbotso.
Amma har yanzu akwai muhimmin bambanci tsakanin:
ABIN DA AKA SANAR
ABIN DA AKA RABA
DA
ABIN DA MANOMI YA SAMU A GASKIYA.
5. ABIN DA BINCIKENMU ZAI BI
A wannan mataki, Alfijir Labarai ba zai yi ikirarin cewa dukkan tallafin ya isa ga manoma ba.
Za mu bi diddigin takamaiman wurare domin gano abin da ya faru a ƙasa.
Za mu duba rabon taki, farashin da manoma suka biya, beneficiaries da kuma damar manoma wajen amfani da ayyukan ban-ruwa.
Daga nan za mu kwatanta bayanan hukuma da abin da manoma suka tabbatar.
6. ABIN DA ZAMU DUBA A SASHE NA GABA
A Fitowa ta gaba, bincikenmu zai shiga wani takamaiman yanki ko ƙaramar hukuma a Kano.
A nan za mu fara neman amsar tambayar da ta fi muhimmanci:
Shin tallafin noma yana ƙarewa ne a matakin sanarwa da ƙaddamarwa, ko kuma yana isa har zuwa gonar manomi?
Mabincika:
Kano State Ministry of Planning and Budget — 2026 Q2 Budget Performance Report
Kano State Budget
Channels Television — Kano Commences Distribution of 90,000 Bags of Fertiliser
Channels Television
Voice of Nigeria — Kano Distributes 90,000 Subsidised Fertiliser Bags
Voice of Nigeria
Voice of Nigeria — NADF Distributes Fertilisers to 25,200 North-West Farmers
Voice of Nigeria
Federal Ministry of Information and National Orientation — NASENI Deploys Solar Irrigation Systems to Transform Agriculture in Kano
NOMA TUSHEN ARZIKI
Mu Bincika. Mu Tambaya. Mu Bayyana Abubuwan da Muka Gano.
Daga Alfijir Labarai
📢 KU CI GABA DA BIN ALFIJIR LABARAI
Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sabbin labarai, rahotanni, bincike, shirye-shirye da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da sauran ƙasashen duniya.
📞 TUNTUBE MU
Domin samun ƙarin bayani, turo mana da labari, haɗin gwiwa, tallace-tallace, ɗaukar nauyin shirye-shirye ko wasu buƙatu:
📱 +234 803 207 7835
📰 Kuna da labari ko wani muhimmin bayani?
Ku turo mana da labaran gaggawa, sanarwar hukumomi, jawabi, sanarwar taro da abubuwan da suka shafi al’umma domin tantancewa da yaɗawa.
🤝 KU YI HAƊIN GWIWA DA MU
Muna maraba da mutane, ƙungiyoyi, hukumomi da ‘yan kasuwa masu sha’awar:
• Haɗin gwiwar kafafen yaɗa labarai
• Tallace-tallace
• Daukar nauyin shirye-shirye
• Haɗin gwiwar kamfanoni da hukumomi
• Rahotanni na musamman da bincike
• Tallata taruka da shirye-shirye
📞 Domin tattaunawa:
+234 803 207 7835
🌐 KU BI MU A KAFAFEN SADA ZUMUNTA
🐦 X (Twitter):
“Ku bi mu a X” https://twitter.com/Musabestseller?s=09
📘 Facebook:
“Ku bi mu a Facebook” https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
🧵 Threads:
“Ku bi mu a Threads” https://www.threads.net/@alfijirlabarai
▶️ YouTube:
“Ku yi Subscibe a YouTube https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
📸 Instagram:
“Ku bi mu a Instagram” https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
📲 SHIGA GROUP WHATSAPP
Ku kasance cikin masu samun sabbin labarai, shirye-shirye, rahotanni da muhimman sanarwa kai tsaye ta WhatsApp.
👇👇
https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f?s=cl&p=a&mlu=4&ilr=4
ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES
Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce
📰 Labarai • Rahotanni • Bincike • Shirye-shirye • Wayar da Kai
© 2026 Alfijir Labarai Media Services
