Shugaban Karamar hukumar Dawakin Tofa Anas Mukhtar Bello Danmaliki ya bayar da Kayan aiki ga Jami’an Vigilantee na jihar kano reshen karamar hukumar Dawakin Tofa domin tabbatar da inganta harkokin tsaron rayuka da dukiyoyin Al’umma.
Danmaliki ya bayar da Yadin Uniform, Takalmi da kuma Belt da Hula tare da Kudin Dinkin Uniform Naira dubu 20 ga dukkannin Jami’an Vigilantee 148 a karamar hukumar Dawakin Tofa.
Yace, ya bayar da Kayan ne domin karfafa musu Gwiwa wajen gudanar da aiki ba tare da rashin samun isassun kayan aikin da suke bukata ba.
Daga nan yayi Alkawarin bayar da Alawus na Naira dubu 20 ga Jami’an Vigilantee na karamar hukumar Dawakin Tofa a dukkannin karshen wata don sake karfafa musu Gwiwa wajen taimakawa harkokin tsaro a yankin .
A nasa bangaren Babban Kwamandan Vigilantee na kano Alhaji Shehu Rabi’u ya yaba tare da mika Godiya ga Shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa Anas Mukhtar Bello Danmaliki bisa yanda ya samar Wanda jami’an Vigilantee abubuwan da suke bukata.
Daga nan yayi kira ga yan Vigilantee na karamar hukumar Dawakin Tofa dasu baiwa jami’an tsaro hadin kai wajen taimakawa harkokin tsaro a yankin.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan ๐
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group ๐๐
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
