UWAR JIKI: PRIMARY HEALTHCARE A JIHAR KANO — INA KUƊADEN LAFIYA SUKE ZUWA?

IMG 192510 18926 1789755934783

Bincike na Musamman daga Alfijir Labarai — 2026

 

Primary Healthcare shi ne matakin farko da mafi yawan jama’a ke dogaro da shi wajen samun kulawar lafiya.

 

A cikin kasafin kudin Jihar Kano na 2026, an ware N14.918 biliyan ga Primary Health Care Management Board (PHCMB).

 

Rahoton aiwatar da kasafin kudi na zangon biyu na shekarar 2026, wanda Gwamnatin Kano ta wallafa a hukumance, ya nuna cewa daga watan Janairu zuwa Yuni an rubuta kashe N5.646 biliyan, wanda ya kai 37.8 cikin 100 na kasafin.

 

Rahoton ya kuma nuna cewa an ware N12.901 biliyan domin babban jarin PHC, daga ciki an rubuta kashe N4.993 biliyan, wato 38.7 cikin 100 zuwa karshen Yuni.

 

Gina da samar da asibitoci da cibiyoyin lafiya

 

A karkashin babban jarin PHC, an ware N2.598 biliyan domin gina ko samar da asibitoci da cibiyoyin lafiya.

 

Zuwa karshen Yuni, rahoton ya nuna an kashe N862.625 miliyan, wato 33.2 cikin 100.

 

Gyaran asibitoci da cibiyoyin lafiya

 

An kuma ware N6.015 biliyan domin rehabilitation da repairs na asibitoci da cibiyoyin lafiya.

 

Rahoton Q2 ya nuna an kashe N2.413 biliyan, wato 40.1 cikin 100 zuwa Yuni.

 

A bangaren da ya shafi renovation da maintenance na Primary Healthcare facilities, an ware N472.5 miliyan, kuma an rubuta kashe N234.5 miliyan, wato 49.6 cikin 100.

 

Kwajele da Fanda: ayyuka biyu da suka jawo hankalin bincikenmu

 

A cikin jerin ayyukan PHC kai tsaye, rahoton ya nuna:

 

N100m — Construction of Primary Healthcare Centre in Kwajele Town, Sumaila LGA.

 

Rahoton Q2 ya nuna 0% expenditure a kan wannan aikin zuwa karshen Yuni.

 

Haka kuma:

 

N100m — Upgrade of Fanda Primary Health Centre, Albasu LGA.

 

Rahoton ya kuma nuna 0% expenditure a kan wannan aikin zuwa karshen Yuni.

 

Wadannan alkaluma ba su tabbatar da cewa ayyukan ba su fara ba. Abin da suka tabbatar shi ne cewa ba a nuna expenditure a karkashin wadannan takamaiman layukan ayyukan a rahoton Q2 ba.

 

Saboda haka, Kwajele da Fanda za su kasance cikin wuraren farko da Alfijir Labarai zai nemi ƙarin bayani a kansu.

 

Magunguna: ƙarin cibiyoyi 100

 

Gwamnatin Kano ta kuma ware N192.21m domin fadada Drug Revolving Fund zuwa karin cibiyoyi 100 domin kara samun ingantattun magunguna.

 

Rahoton Q2 ya nuna 0% expenditure a kan wannan takamaiman aikin zuwa Yuni.

 

Wannan ya haifar da tambayar bincike:

 

Yaushe za a fara aiwatar da wannan fadada shirin, kuma wadanne cibiyoyi ne za su amfana?

 

Referral system

 

An ware N10m domin karfafa tsarin referral daga Primary Healthcare Centres.

 

Rahoton Q2 ya nuna 0% expenditure a kan wannan layin zuwa Yuni.

 

Wannan zai zama muhimmin bangare na bincikenmu, saboda PHC ba koyaushe take iya kula da dukkan matsalolin lafiya ba. Lokacin da bukatar referral ta taso, tsarin kai mara lafiya zuwa cibiyar da ta dace yana da muhimmanci.

 

Laboratory services

 

An ware N20m domin coordination of laboratory services a matakin jiha da kananan hukumomi.

 

Rahoton ya nuna 0% expenditure zuwa Yuni.

 

Saboda haka za mu bincika abin da ake samu a PHCs:

 

Wadanne gwaje-gwaje ake iya yi?

 

Wadanne ba a iya yi?

 

Ina ake kai marasa lafiya idan ba a iya yin gwajin?

 

Kuma nawa ne marasa lafiya ke kashewa?

 

Lafiyar mata da yara

 

Bincikenmu zai kuma bi kudaden da aka ware domin lafiyar mata da yara.

 

Misali, an ware N150.56m domin Child Birth Spacing Programme, inda aka nuna kashe N50m, wato 33.2%.

 

An ware N40m domin Integrated Maternal, Newborn and Child Health, amma rahoton ya nuna 0% expenditure a kan wannan layin zuwa Yuni.

 

An kuma ware N50m domin Active Case Finding of Severe Acute Malnutrition, inda rahoton ya nuna 0% expenditure.

 

A bangaren Nutrition Corners a kananan hukumomi 42, an ware N200.5m, kuma an nuna kashe N100m, wato 49.9%.

 

Rigakafi

 

Routine Immunisation Programme na daga cikin manyan layukan kasafin.

 

An ware N2.912bn, kuma rahoton ya nuna an kashe N1.544bn, wato 53% zuwa karshen Yuni.

 

Wannan zai sa mu tambayi:

 

Shin kudaden sun sauya yadda ake samar da rigakafi a PHCs?

 

Shin ana samun alluran rigakafi a lokacin da ake bukata?

 

Kuma yaya rabon su yake tsakanin birane da karkara?

 

Abin da binciken Alfijir Labarai zai yi yanzu

 

Ba za mu tsaya kan alkaluman kasafin kudi kawai ba.

 

Za mu bi wannan hanya:

 

Kasafi → Aiki → Wuri → Tabbatar da abin da ke kasa → Jama’a → Ma’aikatan lafiya → Amsar gwamnati.

 

Za mu fara da Kwajele, Sumaila da Fanda, Albasu, sannan mu kara wasu PHCs daga cikin ayyukan da aka ware kudade domin gyara, kayan aiki, magunguna da sauran ayyukan kiwon lafiya.

 

Tambayar bincikenmu ita ce:

 

Idan gwamnati ta ware kudade domin Primary Healthcare, me jama’ar Kano suke gani a zahiri a cibiyoyin lafiyarsu?

 

Alfijir Labarai zai ci gaba da bibiyar wannan batu daga takardun kasafi zuwa cibiyoyin lafiya da kuma mutanen da suke amfani da su.

 

Tushen farko: Kano State Government, Q2 2026 Budget Performance Report, musamman sassan Primary Healthcare na shafuka 49–52. Rahoton ya bayyana cewa an shirya shi ne domin nuna kasafin 2026, kashe-kashen Q2 da na shekara zuwa yanzu.

 

📢 KU CI GABA DA BIN ALFIJIR LABARAI

 

Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sabbin labarai, rahotanni, bincike, shirye-shirye da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

 

📞 TUNTUBE MU

 

Domin samun ƙarin bayani, turo mana da labari, haɗin gwiwa, tallace-tallace, ɗaukar nauyin shirye-shirye ko wasu buƙatu:

 

📱 +234 803 207 7835

 

📰 Kuna da labari ko wani muhimmin bayani?

Ku turo mana da labaran gaggawa, sanarwar hukumomi, jawabi, sanarwar taro da abubuwan da suka shafi al’umma domin tantancewa da yaɗawa.

 

🤝 KU YI HAƊIN GWIWA DA MU

 

Muna maraba da mutane, ƙungiyoyi, hukumomi da ‘yan kasuwa masu sha’awar:

 

• Haɗin gwiwar kafafen yaɗa labarai

• Tallace-tallace

• Daukar nauyin shirye-shirye

• Haɗin gwiwar kamfanoni da hukumomi

• Rahotanni na musamman da bincike

• Tallata taruka da shirye-shirye

 

📞 Domin tattaunawa:

+234 803 207 7835

 

🌐 KU BI MU A KAFAFEN SADA ZUMUNTA

 

🐦 X (Twitter):

 

“Ku bi mu a X” https://twitter.com/Musabestseller?s=09

 

📘 Facebook:

 

“Ku bi mu a Facebook” https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

🧵 Threads:

 

“Ku bi mu a Threads” https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

▶️ YouTube:

 

“Ku yi Subscibe a YouTube https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

📸 Instagram:

 

“Ku bi mu a Instagram” https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

📲 SHIGA GROUP WHATSAPP

 

Ku kasance cikin masu samun sabbin labarai, shirye-shirye, rahotanni da muhimman sanarwa kai tsaye ta WhatsApp.

 

👇👇

https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f?s=cl&p=a&mlu=4&ilr=4

 

ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES

 

Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce

 

📰 Labarai • Rahotanni • Bincike • Shirye-shirye • Wayar da Kai

 

© 2026 Alfijir Labarai Media Services

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *