Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Jihar Kano ta tabbatar da Alhaji Muhammad Sani Abacha a matsayin ɗan takararta na kujerar gwamnan Jihar Kano a zaɓen 2027.
Shugaban PDP na Jihar Kano, Injiniya Dr. Bello Gambo Bichi, ne ya bayyana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a Kano.
Matakin ya biyo bayan janyewar Muhammad Bello Dalha, wanda ya lashe zaɓen fidda-gwani na farko na PDP a jihar. Bayan janyewarsa, jam’iyyar ta gudanar da sabon zaɓen fid-da-gwani na maye gurbin ɗan takara, inda Muhammad Sani Abacha ya samu tikitin jam’iyyar.
A yayin taron, manyan jiga-jigan PDP da masu neman kujerun Majalisar Tarayya, da kuma sauran masu ruwa da tsaki daga ƙananan hukumomi 44 na jihar, sun nuna goyon baya ga Abacha tare da jaddada buƙatar haɗin kan jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.
Shugabannin jam’iyyar sun bayyana cewa haɗin kan ɓangarorin PDP na daga cikin matakan da ake ɗauka domin ƙarfafa jam’iyyar da kuma tabbatar da cikakken goyon baya ga ɗan takarar gwamna.
An kuma bayyana cewa Yusuf Ado Kibiya zai kasance abokin takarar Muhammad Sani Abacha na mataimakin gwamna, a wani ɓangare na ƙoƙarin haɗa kan ɓangarorin jam’iyyar a jihar.
PDP ta ce za ta ci gaba da aiki wajen ƙarfafa haɗin kai tsakanin shugabanni, ’yan takara da sauran masu ruwa da tsaki domin tunkarar zaɓen 2027 cikin haɗin kai.
ALFIJIR LABARAI
Accurate • Timely • Trusted
📢 KU CI GABA DA BIN ALFIJIR LABARAI
Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sabbin labarai, rahotanni, bincike, shirye-shirye da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da sauran ƙasashen duniya.
📞 TUNTUBE MU
Domin samun ƙarin bayani, turo mana da labari, haɗin gwiwa, tallace-tallace, ɗaukar nauyin shirye-shirye ko wasu buƙatu:
📱 +234 803 207 7835
📰 Kuna da labari ko wani muhimmin bayani?
Ku turo mana da labaran gaggawa, sanarwar hukumomi, jawabi, sanarwar taro da abubuwan da suka shafi al’umma domin tantancewa da yaɗawa.
🤝 KU YI HAƊIN GWIWA DA MU
Muna maraba da mutane, ƙungiyoyi, hukumomi da ‘yan kasuwa masu sha’awar:
• Haɗin gwiwar kafafen yaɗa labarai
• Tallace-tallace
• Daukar nauyin shirye-shirye
• Haɗin gwiwar kamfanoni da hukumomi
• Rahotanni na musamman da bincike
• Tallata taruka da shirye-shirye
📞 Domin tattaunawa:
+234 803 207 7835
🌐 KU BI MU A KAFAFEN SADA ZUMUNTA
🐦 X (Twitter):
“Ku bi mu a X” https://twitter.com/Musabestseller?s=09
📘 Facebook:
“Ku bi mu a Facebook” https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
🧵 Threads:
“Ku bi mu a Threads” https://www.threads.net/@alfijirlabarai
▶️ YouTube:
“Ku yi Subscibe a YouTube https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
📸 Instagram:
“Ku bi mu a Instagram” https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
📲 SHIGA GROUP WHATSAPP
Ku kasance cikin masu samun sabbin labarai, shirye-shirye, rahotanni da muhimman sanarwa kai tsaye ta WhatsApp.
👇👇
https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f?s=cl&p=a&mlu=4&ilr=4
ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES
Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce
📰 Labarai • Rahotanni • Bincike • Shirye-shirye • Wayar da Kai
© 2026 Alfijir Labarai Media Services
