TAIMAKO
Wani attajiri a Jihar Kano, wanda ya zaɓi ɓoye sunansa, ya bayar da gudummawar buhunan siminti 900 domin tallafa wa aikin gina masallacin Hukumar Shari’a da ke lamba 1, kan titin Abdullahi Bayero a Kano, wanda aka bayyana da suna Commission Sadaka.
Gudummawar ta fito ne bayan attajirin ya ga ana gudanar da aikin ginin masallacin, inda ya yanke shawarar tallafa wa aikin ba tare da ya sanar da kowa ba.
WAKILINSA YA BAYYANA CEWA BA WANNAN NE KARON FARKO BA
Da yake zantawa da Alfijir Labarai, wakilin attajirin ya bayyana cewa kaima sheda ne tunda a gabanka aka kawo motar da ke ɗauke da buhunan simintin 900 a ranar Litinin.
A cewarsa, wannan ba shi ne karon farko da attajirin ke tallafa wa ayyukan alheri ba. Ya ce duk inda attajirin ya ga ana gina masallaci ko makaranta, ko kuma ya samu labarin ana gudanar da irin wannan aiki, yakan bayar da gudummawarsa domin taimakawa wajen ci gaba da aikin.
Wakilin ya ƙara da cewa shi da kansa yake raka wasu daga cikin motocin da ke kai irin waɗannan kayayyakin tallafi zuwa wuraren da ake gudanar da ayyukan alherin.
Ya tabbatar wa Alfijir Labarai cewa ya raka motoci sama da 20, kowacce ɗauke da buhunan siminti 900, a matsayin gudummawar da ake kaiwa wurare daban-daban. A cewarsa, ana gudanar da waɗannan ayyukan ne ba tare da bayyana sunan attajirin ba.
DARASI DAGA WANNAN ATTAJIRI
Akwai darussa masu muhimmanci da za a koya daga wannan lamari.
Na farko: Ba sai an roƙi mutum ba kafin ya taimaka. Idan mutum ya ga wata buƙata da zai iya taimakawa wajen magancewa, zai iya ɗaukar mataki cikin hikima da sanin ya kamata. Wannan na nuna muhimmancin lura da buƙatun al’umma da kuma ɗaukar matakin taimakawa idan hali ya ba da dama.
Na biyu: Ba sai an bayyana sunan mai bayar da gudummawa ba kafin alheri ya yi tasiri. Wannan attajiri ya zaɓi gudanar da ayyukansa na alheri ba tare da neman a san shi ba. Ya kamata a mutunta wannan zaɓi, domin taimako ba ya rasa muhimmancinsa saboda an bayar da shi a ɓoye.
Na uku: Ya kamata dukiya ta zama hanyar amfanar da al’umma. Masu hannu da shuni suna da damar amfani da arzikin da Allah Ya hore musu wajen tallafa wa ayyukan da za su amfani jama’a. Musamman ayyukan da amfaninsu zai ci gaba na dogon lokaci, kamar gina masallatai da makarantu.
Wannan lamari ya tunatar da mu cewa taimakon al’umma ba sai da hayaniya ko neman yabo ba. Abin da ya fi muhimmanci shi ne kyakkyawar niyya, bayar da gudummawa gwargwadon iko, da kuma amfanin da jama’a za su samu.
KIRA GA MASU HANNU DA SHUNI SU YI KOYI
Alfijir Labarai na kira ga masu hannu da shuni da su yi koyi da wannan bawan Allah ta hanyar tallafa wa ayyukan alheri gwargwadon ƙarfinsu, musamman gina masallatai, makarantu da sauran ayyukan da za su amfani al’umma.
Muna fatan wannan misali zai zaburar da sauran masu arziki su yi amfani da dukiyarsu wajen inganta rayuwar jama’a, tare da mutunta waɗanda suka zaɓi gudanar da ayyukan alherinsu a ɓoye.
📢 KU BIBIYI ALFIJIR LABARAI
Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sahihan labarai, rahotanni, bincike da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da duniya.
📩 TUNTUƁA DA HAƊIN GWIWA
WhatsApp: +234 0701 111 3809
KIRA: +234 803 207 7835
🌐 KAFAFEFENMU
X: https://twitter.com/Musabestseller?s=09
Facebook: https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
Threads: https://www.threads.net/@alfijirlabarai
YouTube: https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Instagram: https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
📲 WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f
ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES
Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce
© 2026 Alfijir Labarai Media Services
