Kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta, a unguwar Jaba Kano, ta umarci Mawaki Ado Gwanja, ya dawo da motar da ya tafi yin dani tsawon makomni Uku bai dawo da ita ba.
Alfijir labarai ta rawaito Ado Gwanja, ya siyi motar ne a hannun Mustapha Adamu wanda shine ya shigar da karar, amma Gwanjan yayi zargin cewa motar bata da lafiya, In da aka umarci Mustapha, ya gyara masa, kuma bayan ya gyara ne, kotun ta ba wa Ado Gwanja, don yayi gwaji , sai daga bisani ake zargin yaki dawo wa da motar tsawon lokaci.
Mai karar ya shaida wa kotun cewar Yana bin Gwanja sauran kudi kimanin naira Dubu 500,000 shi yasa yayi kararsa.
A zaman kotun da ya gabata lauyan Mai karar ya roki Kotun, ta bayar da umarnin kamo Ado Gwanja.
Alkalin kotun Mai shari’a Malam Rabi’u Yahaya, ya umarci, Ado Gwanja, ya dawo da motar a ranar 12 ga watan Disamba 2024, In da kotun ta ce zata juyar da Shari’ar zuwa babbar kotun shari’ar addinin musulinci ta Sabon gari.
Idon Gari
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj
