Wata Sabuwa! Wani Dattijo Ya Sare Hannayen Alkalin Kotu a Adamawa Yana Tsaka Da Shari’a

IMG 135158 09926 1788958350722

Wani dattijo mai shekaru 87 ya kai hari kan alkalin Kotun Yankin Mayo-Ine da ke karamar hukumar Fufore a jihar Adamawa, inda ya sare hannayensa da adda.

 

Dattijon mai suna Dahiru Garba, mazaunin kauyen Korawa da ke gundumar Mayo-Ine, ya aikata hakan ne a ranar 31 ga watan Agusta, yayin da alkalin, Dauda Hamman, ke sauraron karar da aka shigar tsakaninsa da wani Ismail Yusuf.

 

Rahotanni sun ce Dahiru ya yi amfani da adda wajen sare hannayen alkalin, lamarin da ya jikkata shi sosai.

 

Bayan kama shi, an gurfanar da Dahiru a gaban Babbar Kotun Majistare ta Farko dake Yola a ranar Litinin, inda aka karanta masa tuhumar haddasa mummunan rauni, laifin da ya sabawa sashe na 219 na dokar hukunta laifuka ta jihar Adamawa ta shekarar 2018.

 

Dahiru ya amsa laifin da ake tuhumarsa dashi, yana mai cewa shaidan ne ya jefa shi cikin aikata hakan, tare da bayyana matukar nadamarsa.

 

Mai gabatar da kara, ASP Zakka Musa, ya shaida wa kotun cewa an mayar da binciken lamarin daga hedikwatar ‘yan sanda ta Fufore zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar a ranar 4 ga Satumba.

 

Ya ce alkalin ya kai rahoton harin ne a ofishin ‘yan sanda na Mayo-Ine, bayan Dahiru ya sare shi da adda a lokacin da yake gudanar da shari’ar.

 

Alkalin Babbar Kotun Majistare ta Farko, Ismail Bello Shelleng, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare Dahiru a gidan gyaran hali da ke Yola.

 

Kotun ta ɗage cigaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 17 ga Satumba, 2026.

 

Adamawa Reporters

 

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

 

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

 

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

 

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

 

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *