Ƙalubale Da Cigaban Iran: Dubu 1, A Najeriya Daidai Take Da Dubu 30 A Iran Duk Da Takunkumai Da Suka Kewayeta

IMG 20260725 WA1675

Daga Aminu Bala Madobi

Mahangar Cigaban Najeriya A Ina Ya Maƙale? Ina Gizo Ke Saƙar?

Kuɗin ƙasar Iran na daga cikin kuɗaɗen ƙasashe da suka fi fuskantar matsananciyar faɗuwar daraja a duniya. Kididdiga ta bayyana cewa Naira 1,000 ta Najeriya na iya yin daidai da kusan Naira dubu 30 idan aka canza ta zuwa kuɗin Iran, lamarin da ke nuna yadda darajar kuɗin ƙasar ta ragu sosai idan aka kwatanta da wasu kuɗaɗen duniya.

Duk da wannan raunin darajar kuɗi, ana cewa idan mutum ya mallaki Miliyan 100 na kuɗin Iran, idan aka canza su zuwa Naira za su zama kusan Miliyan 3 da dubu 300. Sai dai masana tattalin arziƙi na jaddada cewa darajar kuɗi kaɗai ba ita ce ke tantance ƙarfin tattalin arziƙin ƙasa ba, domin farashin kayayyaki da albashi a cikin ƙasar suna tafiya ne da tsarin tattalin arziƙinta.

Iran ta ci gaba da samar da muhimman ayyukan more rayuwa kamar ilimi, lafiya, tituna, wutar lantarki, tsaro da kuma bunƙasa fasahohi daban-daban. Wannan ya kasance duk da cewa ƙasar ta shafe sama da shekaru 40 tana fuskantar takunkuman tattalin arziƙi daga Amurka da wasu ƙasashen duniya, lamarin da ya takaita harkokin kasuwanci da hulɗarta da ƙasashe da dama.

Masu nazari na ganin cewa juriyar Iran wajen ci gaba da bunƙasa wasu fannoni duk da takunkuman da ake mata na ɗaya daga cikin abubuwan da suka ja hankalin duniya. Duk da ƙalubalen da take fuskanta, ƙasar ta ci gaba da saka jari a fannoni masu muhimmanci domin biyan bukatun al’ummarta da kuma haɓaka fasahohin cikin gida.

Akwai darasi mai girma a nan. Ƙarfin ƙasa ba wai darajar kuɗinta kaɗai ake aunawa ba, ana kuma kallon yadda gwamnati ke samar wa al’umma ilimi, lafiya, tsaro, wutar lantarki, ayyukan yi da sauƙin rayuwa. Idan waɗannan abubuwa suna aiki, talaka kan samu damar rayuwa cikin kwanciyar hankali ko da kuɗin ƙasar bai fi na wasu ƙasashe ƙarfi ba.

A Najeriya kuwa, abin da ya fi damun talakawa shi ne tsadar rayuwa da raguwar ƙarfin sayen kuɗi.
Farashin abinci, sufuri, magunguna da sauran buƙatun yau da kullum na ci gaba da hauhawa, yayin da albashin mutane da dama bai ƙaru daidai da wannan yanayi ba.

Wannan ne ya sa iyalai da dama ke fama da matsin tattalin arziƙi duk da ƙoƙarin da ake yi na aiwatar da wasu tsare-tsare.

Don haka, babban buri ba wai a samu kuɗi mai yawa  ba ne, illa a gina tattalin arziƙin da zai sauƙaƙa rayuwar jama’a. Talaka yana buƙatar ya iya cin abinci, samun magani, ilimi mai inganci, wutar lantarki, tsaro da aikin yi cikin sauƙi. Idan aka cimma hakan, rayuwar al’umma za ta inganta, kuma ci gaban ƙasa zai kasance abin da kowa zai amfana da shi.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *