Ƙasar Rasha ta yi kira ga Amurka da Isra’ila su daina kai hare-hare kan Iran

FB IMG 1773331117857

Rasha ta yi kira ga Amurka da Isra’ila da su dakatar da kai hare-hare kan Iran, tana mai cewa ya kamata su koma teburin tattaunawa domin warware sabanin da ke tsakaninsu.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha, Maria Zakharova, ta bayyana cewa halin jin kai a yankin na kara tabarbarewa, yayin da rikicin ke ci gaba da ƙara tsananta.

Ta ce ƙara tashin hankali a rikicin na daga cikin abubuwan da ke haddasa damuwa mai tsanani ga al’ummar yankin da kuma duniya baki ɗaya.

“Rasha za ta ci gaba da yin duk abin da za ta iya domin ganin an kawo ƙarshen rikicin a yankin Gabas ta Tsakiya,” in ji ta.

Ta kuma kara da cewa rahotannin hukuma sun nuna cewa mutane da dama sun jikkata sakamakon hare-haren da aka kai a Iran.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *