Ƙarshen Alewa: NDLEA ta kama tsohon dillalin hodar iblis da ya fake da sana’ar siyar da shayi

FB IMG 1788712763754

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama wani tsohon dillalin hodar iblis da aka taba yanke wa hukuncin zaman gidan yari, bisa zargin shirya safarar hodar iblis zuwa Saudiyya.

 

Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya ce an kama mutumin mai suna Dunu Bethel Ebubechukwu, mai shekaru 34, a wani samame da aka gudanar a yankin Ojo na Legas ranar Juma’a, 4 ga Satumba, 2026, yayin da yake fakewa da sana’ar siyar da shayi.

 

A cewar NDLEA, an gano cewa Ebubechukwu an taba kama shi a shekarar 2011 a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da gram 900 na hodar iblis da gram 130 na heroin, lokacin da yake kokarin tafiya Austria.

 

Hukumar ta ce an gurfanar da shi, aka yanke masa hukuncin shekaru biyar a gidan yari, amma daga baya ya sauya suna tare da komawa harkar fataucin miyagun kwayoyi.

 

NDLEA ta kuma ce binciken gidan wanda ake zargin ya kai ga gano wasu cajar wayoyi da aka cire musu sassan ciki domin amfani da su wajen boye miyagun kwayoyi.

 

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

 

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

 

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

 

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

 

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *