Gwamnatin Jihar Kano ta umarci dukkan ma’aikatanta da su sabunta bayanan kansu da na aikinsu ta hanyar manhajar Kano Integrated Personal and Payroll Information System (KIPPS).
Umarnin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano, ta hannun Daraktar Human Resource Development, ta fitar a ranar 4 ga Satumba, 2026.
Sanarwar ta ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na tabbatar da ingantaccen tsarin kula da albarkatun ɗan Adam, tare da samar da sahihan bayanai da za a iya amfani da su wajen gudanar da harkokin ma’aikata cikin sauƙi da inganci.
Gwamnatin ta kuma umarci dukkan Ma’aikatu, Hukumomi da Sassan Gwamnati (MDAs) da su taimaka wajen ganin ma’aikatansu sun shiga manhajar KIPPS tare da sabunta bayanan Biodata da sauran bayanan da suka shafi aikinsu.
Sanarwar ta bayyana cewa dole ne dukkan ma’aikatan gwamnatin jihar su kammala sabunta bayanansu kafin ko zuwa ranar 30 ga Satumba, 2026, domin tabbatar da cewa bayanan da gwamnati ke da su sun kasance na zamani kuma sahihai.
Sanarwar mai dauke da sa hannun babban Sakataren na hukumar ma’aikatan jihar Sabi’u Shuaibu Muhammad, inda aka kuma bukaci dukkan hukumomin da abin ya shafa da su bai wa wannan umarni cikakken goyon bayan da ya kamata da kuma isar da saƙon ga dukkan ma’aikata domin a kammala aikin cikin wa’adin da aka sanya.

Head Of Services

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
